Yarbawa ne za su karbi mulkin Najeriya a 2023 - Olayiwola

Yarbawa ne za su karbi mulkin Najeriya a 2023 - Olayiwola

Wani babban malamin addinin Kirista mazaunin birnin Abeokuta a jihar Ogun, Dr Olayiwaola Samson Mercy, ya ce a yanzu lokaci ne yankin Kudu maso Yammacin Najeriya ya samar da shugaban kasa wanda zai karbi akalar jagoranci a shekarar 2023.

Duk da irin hankoron sauran yankunan Najeriya na ganin cewa akalar mulkin kasar nan ta koma hannun su a 2023, Dr Samson ya ce a yanzu ne lokacin da ya yi daidai yankin kabilar Yarbawa da ya kasance Kudu maso Yamma ya jagoranci kasar.

A yayin haka Dr Olayiwola yana tunatar da shugabannin kabilar Yarbawa da su tumke damarar su wajen fafata bakin gumurzu na karbar akalar jagorancin kasar a 2023, lamarin da ya yankin Arewa ba zai yi wa sauran yankunan kasar rangwami ba na ganin ya ci gaba da mulkar kasar.

Furucin malamin wanda ya kasance jagoran Cocin Christ Divine Churches International, na zuwa ne yayin gabatar da hudubarsa ta ranar Lahadi a birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Ya ce duk da irin gumurzu da yankunan kasar nan za su yi wajen karkatar da akalar jagorancin kasar garesu a 2023, hakan ba zai haifar da rabuwar kai ta al'umma ba illa iyaka kara hadin kai tamkar tsintsiya madauri daya.

KARANTA KUMA: N200m gwamnati ta ke batar wa a kowane wata domin samar da haske a titunan birnin Kano

Dr Olayiwola yayin gargadin al'ummar Najeriya kan zama lafiya da aminci na hadin kai, ya ce babu makawa kasar nan ba za ta gushe ba wajen yunkura wa zuwa mataki na ci gaba a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Haka zalika cikin yakini da kyautata zato, Dr Olayiwola ya ce yankin kabilar Yarbawa na Kudu maso Yammacin Najeriya zai ci gajiyar kujerar Buhari bayan kammala wa'adinsa a 2023.

Ya kuma kyautata zato da cewa, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, zai kwashe lafiya tare da bai wa maradansa kunya wanda babu shakka zai taka muhimmiyar rawar gani a siyasar 2023.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel