Tinubu zai dora a kan tubalin Buhari idan ya zama shugaban kasa a 2023 - Razaq

Tinubu zai dora a kan tubalin Buhari idan ya zama shugaban kasa a 2023 - Razaq

Babban jigo kuma kanwa uwar gamin jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, zai dora a kan tubali na salon mulki wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke kai a yanzu idan ya ci gajiyarsa a 2023.

Wannan furuci ya fito daga bakin jigon APC, Lanre Razak, wanda kuma ya kasance daya daga cikin na hannun daman Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas.

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa, Razak ya jaddada yankininsa da cewa babu shakka Tinubu yana da duk wata cikakkiyar cancanta ta cin gajiyar mulkin kasar nan a hannun Buhari a 2023.

Razak ya hikaito irin muhimmiyar rawar da Tinubu ya taka wajen tabbatar da nasarar shugaban kasa Buhari a 2015 tare da lallasa babbar jam'iyyar hamayya ta kasar wato PDP, lamarin da ya ce ya dawo wa da kasar martabar dimokuradiyya.

A wani rahoto da jaridar BBC Hausa ta ruwaito a watan Yulin da ya gabata, Tinubu ya yi watsi da yunkurin wasu kungiyoyi masu tallata shi a matsayin mai sansanar kujerar shugaban kasar Najeriya a 2023.

KARANTA KUMA: Jihar Jigawa da Neja za su fara biyan mafi karancin albashi na N30,000 a karshen watan Oktoba

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana hakan ne a shafin sada zumunta na zamani wato Twitter, inda ya ce sam bai da wata alaka da kungiyar mai sunan 'Asiwaju Reloaded Ambassadors' Nigeria'.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel