'Yan Najeriya za su more a gwamnatin Buhari kafin 2023 - Tunde Bakare

'Yan Najeriya za su more a gwamnatin Buhari kafin 2023 - Tunde Bakare

Babban limamin cocin Latter Rain Assembly, Fasto Tunde Bakare, a ranar Lahadi 6 ga watan Oktoba, ya yi fadin cewa, 'yan Najeriya su sha kurimin su domin kuwa za su sharbi romon a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari gabanin saukarsa a 2023.

A rahoton da jaridar Daily Trust ta ruwaito, Fasto Bakare ya yi ambato hakan a cocinsa da ke birnin Iko na jihar Legas, inda ya gabatar da hudubarsa a kan murnar cikar Najeriya shekaru 59 da samun 'yancin kai.

Babban Faston wanda a 2011 ya kasance abokin takarar shugaban kasa Buhari a tsohuwar jam'iyyar CPC, ya tunatar da 'yan Najeriya cewa neman takarar kujerar shugabancin kasar nan a bude take ga dukkanin kowa ba tare da la'akari da kabilanci ba.

A yayin da ya jaddada cewa Buhari zai fidda kasar nan zuwa tundun mun tsira gabanin ya sauka daga kujerarsa a 2023, Bakare ya gargadi al'ummar kasar da su haramta wa kawunansu adawa da kiyayya a tsakanin juna.

KARANTA KUMA: Jihar Jigawa da Neja za su fara biyan mafi karancin albashi na N30,000 a karshen watan Oktoba

A wani rahoto da jaridar BBC Hausa ta ruwaito a ranar 12 ga watan Janairun 2017, Fasto Bakare wanda ya fito takarar mataimakin shugaban kasa tare da shugaban kasa Buhari a shekarar 2011, ya ce gwamnatin shugaban kasar ta jefa Najeriya a halin ci baya a madadin ci gaba.

A daya daga cikin hudubobin da ya gabatar, Fasto Bakare, gwamnatin Buhari ta gaza zage dantsenta a kan tubalin da aka assasa ta na magance matsalar tsaro, samar da ayyuka da kuma yaki da rashawa, lamarin da ya ce ya jefa kasar a hali na koma baya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel