Boko Haram: An bai wa malamai 30 kwangilar addu'a a Saudiyya

Boko Haram: An bai wa malamai 30 kwangilar addu'a a Saudiyya

Farfesa Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno, ya bai wa wasu malamai kimanin 30 mazauna birnin Makkah na kasar Saudiya, kwangilar gudanar da addu'o'i da kuma dawafi domin rokon Mai Duka ya magance musibar kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram.

Cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau, ya ce gwamnatin Borno ta bai wa wadannan malamai 30 mazauna birnin Makkah kwangilar gudanar da addu'o'i wajen rokon 'Buwayi Gagara Misali' da ya wanzar da aminci a jihar da kuma kasa baki daya.

A cewar Alhaji Gusau, gwamna Zulum ya kulla wannan jarjejeniya da zababbun mutanen 30 mazauna birnin Makkah, domin su dawwama wajen gudanar da addu'o'i da kuma dawafi wato zagayen Ka'aba wajen rokon Mai Kowa Mai Komai da ya saukar da aminci a jihar Borno da kuma kasar nan.

Ya ce malaman 30 da aka bai wa wannan kwangila sun fito ne daga jihohin Borno, Katsina, Zamfara, Kano da kuma wasu sassa na yankin Arewa maso Gabas, da suka shafe fiye da shekaru 10 na zama a kasar Saudiya.

Cikin wadanda gwamnatin jihar Bornon ta kulla yarjejeniyar da su sun hadar da wani dattijo da ya shafe kimanin shekaru 40 a farfajiyar masallaci mai alfarma na Ka'aba wajen gudanar da ibada.

KARANTA KUMA: Rashin amincewa da auren jinsi ya sa tsohon firaiministan Birtaniya ya addabi gwamnati na - Jonathan

Jaridar The Punch ta ruwaito kakakin gwamnan yana cewa, an kulla yarjejeniyar tare da malaman 30 yayin da gwamna Zulum ya gana da su a ranar Juma'ar da ta gabata cikin birnin Makkah.

Alkalumma sun tabbatar a cewa ya zuwa ya yanzu kungiyar masu tayar da kaya baya ta Boko Haram ta haura kimanin shekaru da daura damarar ta'addanci a kasar nan musamman yankin Arewa maso Yamma da kuma wasu kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel