Rashin amincewa da auren jinsi ya sa tsohon firaiministan Birtaniya ya addabi gwamnati na - Jonathan

Rashin amincewa da auren jinsi ya sa tsohon firaiministan Birtaniya ya addabi gwamnati na - Jonathan

Tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, ya ce tuhumar da tsohon Firaiministan Birtaniya, David Cameron yayi masa da cewa shi ne ya hana ruwa gudu wajen ceto 'yan matan Chibok, tatsuniya cewa maras tushe.

Haka kuma Mista Cameron ya yi zargin cewa almundahana, sama da fadi da dukkanin wasu miyagun ababe na satar dukiyar talakawa gami da cin hanci da rashawa, sun kasance al'ada a gwamnatin tsohon shugaban kasar Najeriya.

David Cameron wanda ya kasance Firaiministan Birtaniya a yayin da mayakan Boko Haram suka sace 'yan Chibok, yayi zargin cewa tsohon shugban na Najeriya shi ne ya kawo wa gwamnatin Birtaniya tsaiko wajen ceto 'yan Matan a hannun masu ta'adar.

Tsohon Firaiministan na Birtaniya yayi wannan zargi cikin wani littafi da ya wallafa mai lakabin, For The Record, inda ya ce babu shakka hukumominsu sun hango 'yan Matan Chibok a wani kasurgumin daji, sai dai Jonathan yayi likimo da zargin cewa an siyasantar da lamarin ne kurum ba wani abu ba.

Jaridar BBC Hausa ta ruwaito cewa, wannan zargin na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Matan Chibok ke cika kwanaki 2,000 da sace su.

KARANTA KUMA: Sowore: Dalilin da ya sa Buhari ba zai sa baki ba a yanzu - Adesina

Da ya ke yin raddi tare da mayar da martani kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, tsohon shugaban Najeriya Jonathan, ya ce rashin amincewa da auren jinsi da yayi ya sa tsohon firaiministan Birtaniya ya addabi gwamnatinsa.

Jonathan ya ce babu shakka tsohon Firaiminitan Birtaniya, ya yiwa gwamnatinsa barazana game da addabarta biyo bayan sanya hannu a kan dokar haramta auren jinsi a Najeriya a shekarar 2014.

A martanin da mayar wa Mista Cameron a shafinsa na sada zumunta, Jonathan ya bayyana mamaki matuka dangane da wannan kazafi, da cewar babu ta yadda za a yi ya juya baya kan duk wani taimako da ya nema daga kasashen duniya wajen ceto 'yan Matan Chibok.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel