Jonathan: Kowa ya san sakacin ka ya sa aka yi gaba da Matan Chibok – APC

Jonathan: Kowa ya san sakacin ka ya sa aka yi gaba da Matan Chibok – APC

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ba tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan, shawara cewa ya daina damuwa da maidawa Takawaransa na Birtaniya David Cameron martani.

Tsohon Firayim Minista David Cameron na Birtaniya ya fito ya daurawa shugaba Jonathan laifin yin gaba da Yaran makarantar Chibok da aka yi inda yace Jonathan ya hana a kubutar da su.

Dr. Goodluck Jonathan ya yi maza ya kare kansa daga zargin sakaci inda yace wata kullaliya ce dai ta sa David Cameron ya taso shi a gaba. Jam’iyyar APC ta fito ta ba Mista Cameroon gaskiya.

Mai magana da yawun jam’iyyar APC, Lanre Issa-Onilu, yace kowa ya san sakacin Jonathan da ya saba ne ya haddasa cabewar sace matan Chibok da aka yi kwanaki sama da 2000 da su ka wuce.

KU KARANTA: Jonathan ya musanya ikirarin David Cameroon a kan matan Chibok

A wani jawabi da APC ta yi ta bakin Malam Lanre Issa-Onilu ya zargi gwamnatin shugaba Jonathan da yi wa Duniya karya kan yadda sha’anin sace ‘Yan makarantar na Chibok ya wakana.

A Ranar Asabar 5 ga Watan Oktoba, Kakakin jam’iyyar mai mulki yake cewa abin da ya faru ya nuna aya ne game da irin rashin gaskiyar da aka rika tafkawa a lokacin da PDP ta rika mulki.

Issa-Onilu ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja. Jam’iyyar APC ta na zargin gwamnatocin PDP da sace dukiyar Najeriya na shekaru 16 da su ka yi a kan mulkin kasar.

Jonathan dai ya dade ya na musanya zargin laifinsa wajen sace ‘Yan makarantar kwana fiye da 200 da aka yi a lokacin ya na mulki. APC ta hakikance a kan cewa wasa ya yi lokacin da mulki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel