Yadda Lawan da Gbajabiamila za su kerewa kokarin Majalisa ta 8 - Inji Jega

Yadda Lawan da Gbajabiamila za su kerewa kokarin Majalisa ta 8 - Inji Jega

Tsohon shugaban hukumar zabe na kasa na INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira ga majalisar tarayya ta tara a Najeriya ta yi izna da irin kure-kuren da majalisar da ta shude a baya ta rika yi.

Kamar yadda mu ka ji, Attahiru Jega, ya bada shawarar cewa idan wannan majalisar ta na son samun nasara, lallai dole ta yi watsi da rikicin da wancan majalisar ta baya da rika cusa kanta.

Tsohon gwamnan jihar Kwara, Bukola Saraki da kuma Rt. Hon. Yakubu Dogara ne su ka jagoranci majalisa ta takwas, yayin da Ahmed Lawan da kuma Femi Gbajabiamila su ke kan mulki a yanzu.

Farfesa Jega ya yi wannan kira ne a Ranar Juma’a, 4 ga Watan Satumba 2019, lokacin da ake gabatar da wata doguwar takarda mai shafuka 114 kan irin nasarori da kulubalen majalisar baya.

Kungiyar nan ta YIAGA ce ta shirya wannan zama da aka yi a babban birnin tarayya Abuja. Tsohon shugaban na INEC ta na cikin wadanda su ka yi jawabi tare da bada wasu shawarwari.

KU KARANTA: Majalisa ta kara abin da Najeriya za ta kashe a kasafin 2020

Jega yake cewa majalisar da ta gabata ta yi wani irin namijin kokari na kawo kudirori 2, 166 a shekara hudu. Daga ciki an samu 515 da su ka zama doka yayin da wasu su ka shafe wasu dokoki.

Sai dai kuma tsohon shugban hukumar zaben ya ce kawo kudirori kurum ba shi bane abin da za ayi la’akari da shi, Jega yace ya kamata a duba kyawun irin kudirorin da ake gabatarwa a kasar.

Kokari wajen bin diddikin kudirorin da ‘yan majalisar tarayya ke kawowa shi zai hana takarda ta je hannun shugaban kasa ta dawo gaban majalisa saboda wasu kura-kurai inji Attahiru Jega.

Bayan haka kuma, Farfesan ya yi kira ga ‘yan majalisa su fara amfani da a’urori na zamani wajen kada kuri’unsu a lokacin da aka kawo wata muhawara ko zabe a gaban zauren na majalisar kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel