Gwamnoni za su zauna da Shugaba Buhari kan batun kudin gyaran hanya

Gwamnoni za su zauna da Shugaba Buhari kan batun kudin gyaran hanya

Gwamnonin jihohin Najeriya da ke karkashin kungiyar gwamnonin kasar na NGF, su na shirin aika wakilai domin su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan batun kudin tituna.

Kamar yadda mu ke samun labari, gwamnonin su na so shugaba Buhari ya dawo daga rakiyar matakin da ya dauka na kin dawo masu da kudin da su ka kashe a kan gyara hanyoyin tarayya.

Gwamnonin sun kashe kudinsu ne wajen gyaran titunan gwamnatin tarayya da ke jihohinsu. Don haka ne su ke neman a dawo masu da wannan kudi yayin da shugaba Buhari ya murtuke fuska.

Shugaban kasa Buhari dai ya hana a rika biyan gwamnoni wani kudi da sunan gyaran manyan hanyoyin tarayya. Yayin da ake fama da wannan ja-in-ja, majalisa ta goyi bayan shugaban kasar.

GwamnatinBuhari ta bakin Minista Babatunde Fashola ta nemi gwamnonin su daina yi wa titunan gwamnatin tarayya faci tun farko idan har sun san za su nemi a dawo masu da kudinsu.

KU KARANTA: Sanatoci sun amince da karin Biliyan 700 a kasafin kudin 2020

Ministan ayyukan ya sanar da Majalisa cewa gwamnoni sun saba tatsar makudan kudi daga hannun gwamnatin tarayya a duk lokacin da su ka gyara wasu hanyoyin tarayya da ke jihohinsu.

Daga hawan shugaban kasa Buhari kan mulki zuwa yau, jihohi sun nemi a biya su kudin da ya haura Tiriliyan 1 na ayyukan da su ka yi. Wannan ya sa Buhari yace jihohi su daina taba titunan.

Wani gwamna da ya zanta da Manema labarai, ya bayyana cewa su na shirin zama da shugaban kasa a kan wannan batu da kuma maganar yadda ake kasa kudin da kasar ta ke samu duk wata.

“Ina tunani za mu dauki mataki da wuri. Ba dole bane ya zama wani babban zama. Watakila sa’a guda ko biyu za mu yi da shugaban kasar, zai mu kawo masa maganar. Shikenan.” Inji gwamnan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel