Babu ranar kawo karshen mummunan rikicin siyasar Ribas a Najeriya

Babu ranar kawo karshen mummunan rikicin siyasar Ribas a Najeriya

A wani dogon rahoto da wata babbar jaridar Najeriya ta fitar, mun samu labari cewa jiga-jigan siyasan jihar Ribas ba su canza sahu ba, bayan irin abin da ya faru a jihar a zaben bana na 2019.

Jam’iyyar AAC ta shigo gari a Ribas bayan hana APC takara da aka yi a zaben 2019. Ministan sufuri Rotimi Amaechi ne ya labe a cikin tafiyar APC bayan ganin jam’iyyarsa ta shiga matsala.

Tsohon gwamnan na APC ya marawa Biokpomabo Awara baya da kudi da karfinsa a zaben gwamnan da aka yi a Ribas ne bayan yunkurinsu a kotu na kyale APC ta yi takara ya sha kashi.

A daidai lokacin da ake shirin zabe ‘dan takarar mataimakin gwamnan jam’iyyar AAC, Akpo Bomba Yeeh, ya sauya-sheka zuwa PDP. Wannan ya taimaka wajen kara nakasa jam’iyyar adawar.

Sai dai manyan jagororin siyasa a jihar irinsu Magnus Abe, Rotimi Amaechi, Awara Yeeh, da shi kan sa gwamna mai-ci watau Nyesom Wike ba a ga maciji. Tun tuni ake wannan rikici har gobe,

Sai dai alamu su na nuna cewa akwai wani shiri da ake yi tsakanin Sanata Magnus Abe da kuma gwamna Nyesom Wike. Abe ya na cikin wadanda ke gaban rikici da tsohon gwamna Amaechi.

KU KARANTA: Gwamna Wike ya samu nasara a kotun karar zaben 2019

Yunkurin da Amaechi da sauran mutanensa na APC su ka yi na kalubalantar PDP a zaben 2023 ta karkashin kasa da jam’iyyar AAC bai kai ga ci ba. Yanzu uwar jam’iyya ta fara neman yin sulhu.

Sai dai Yaran Magnus Abe sun nuna cewa ba za su amince da duk wani mukamin rikon kwarya da za a ba su ba a shirin da jam’iyyar APC ta ke yi na kafa shugabannin wucen gadi kafin ayi zabe.

Shi kuma gwamna Nyesome Wike ya na ta kara karfi a gida a daidai lokacin da ‘yan adawa ke rikici tsakaninsu. Sai dai shi kan sa Wike ya samu sabani da manyan shugabannin PDP na kasa.

Kwanaki ne Tsohon gwamnan jihar Ribas Rt, Hon. Rotimi Amaechi, ya jaddada aniyarsa na ganin Yankin Kudu maso Gabashin kasar nan sun fito da shugaban kasa domin ba su taba mulki ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel