Dalilin da yasa muke rusa gidajen karuwai da mashaya - Gwamnatin jihar Borno

Dalilin da yasa muke rusa gidajen karuwai da mashaya - Gwamnatin jihar Borno

Babban lauyan jihar Borno kuma kwamishanan Shari'a, Kaka-Shehu Lawan, ya ce rushe-rushen gidajen karuwai da mashaya a da gwamnatin jihar keyi wani mataki ne da suke dauka bisa ga binciken leken asirin jami'an tsaro.

Lawan ya ce a makon da ya gabata kadai, an rusa gidajen karuwai, mashaya da otal akalla ashirin saboda sun sabawa dokokin jihar da ya haramta ayyukansu.

Ya ce uku dafa cikin gidajen an rusa su ne saboda ana amfani da su wajen ajiye kananan yara domin bugar da su da kwaya kafin lalata da su.

A bara, gwamnatin jihar ta rusa mashaya di gidajen karuwai 47 saboda sun zama daban alfasha da munkari a jihar.

KU KARANTA: Sanannun yara 6 masu hannu da shuni a Najeriya

Dokar jihar ta haramta dukkan irin ayyukan karuwanci da mashayar giya a sassan jihar illa barikin sojoji.

Masu gidajen karuwai 47 da aka rusa sun gudanar da zanga-zanga a wani hira da suka gabatarwa manema labarai inda suka bukaci gwamnati ta biyasu kudin gine-ginensu da aka rusa.

A wani labarin mai kama da haka, Jami'an Hisbah na jihar Jigawa ta ce ta kama wata mota kirar Sharon dauke da kwalaben giya 389 a jihar.

Kwamandan Hisbah na jihar, Ibrahim Dahiru, ne ya bayyana hakan yayin wata zantawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai (NAN) a Dutse a ranar Laraba.

Dahiru ya ce an kama motar ne yayin wata sumame misalin karfe 10 a ranar 1 ga watan Oktoba a karamar hukumar Hadejia na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel