Wani gwamnan PDP ya yi nasara a kotun sauraron kararrakin zabe

Wani gwamnan PDP ya yi nasara a kotun sauraron kararrakin zabe

- Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike ya nuna matukar murnarsa akan nasarar da ya samu a kotun sauraron kararrakin zabe

- Gwamnan ya jaddada cewa dama can ba shi da abokin hamayya a zaben 9 ga watan Maris

- Ya jinjinawa kungiyar lauyoyinsa akan aikinsu inda suka ce taimakon Ubangiji ne ya basu nasarar

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike ya ce shi dama tun farko babu wanda suka nemi kujerar shugabancin jihar tare a zaben ranar 9 ga watan Maris.

Gwamna Wike da sauran shuwagabannin jihar Rivers sun garzaya majami'a don mika godiya ga mahalicci akan nasarar da ya yi a kotun sauraron kararrakin zabe.

A yayin maida martani akan hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben da ta tabbatar da nasararsa, Gwamna Wike ya ce duk 'yan jam'iyyar PDP na jihar basu da abokan hamayya.

KU KARANTA: Da arziki a gidan wasu: An binciko wani tsohon gwamna da ya siyarwa kansa motocin gwamnati a rahusa

Ya ce: "Abin haushi ne ace wani ya tashi kwatsam, ya ce ba a yi zabe a jihar Rivers ba. Mu dai mun san bamu da abokan hamayya,"

Gwamna Wike ya ce ba kalubalen 'yan hamayya ba zai taba janye masa hankali ba don haka zai cigaba da kare ra'ayin jihar Rivers.

"Hankali na ba zai taba daukewa ba. Zan yi komai amma cikin abinda mutanen jihar Rivers ke so," in ji shi.

Gwamnan jihar Rivers din ya nuna farincikinsa akan adalcin da aka yi wa shari'ar. Ya kara da mika godiyarsa ga kungiyar lauyoyinsa akan jajircewarsu.

Ahmed Raji, ya danganta nasarar da taimakon Ubangiji. Ya ce tun farko ubangiji ne ya yi masa jagora.

Raji yace Ubangiji ne ya sakawa jajircewar kungiyar lauyoyin da nasarar nan. Ya ce hukuncin tabbaci ne na shari'a akan zaben mutanen jihar Rivers.

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus ya taya Gwamna Wike murnar nasarar.

Ya ce anyi adalci ga mutanen jihar Rivers ta hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel