Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sace makiyaya shida a Adamawa

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sace makiyaya shida a Adamawa

Wasu mutane dauke da makamai sun sace makiyaya shida a jihar Adamawa.

Wani majiya daga garin ya shaidawa Sahara Reporters cewa a ranar Asabar 'yan bindigan sun shigo kauyen Gurin a karamar hukumar Fufore inda suka yi awon gaba da matasa shida.

Majiyar ta kara da cewa an sace matasan ne a kan hanyar Fufore zuwa Gurin a safiyar Asabar.

A cewar majiyar, wadanda aka sace suna kiwon shanunsu a wata fili yayin da masu garkuwa da mutanen suka bullo suka yi awon gaba da su.

Kauyen Gurin yana kusa da wani rafi ne da ya raba Najeriya da Kamaru a kan iyakar Kudu maso Gabshin Adamawa.

DUBA WANNAN: An kama wani gardi da ya yi basaja a matsayin karuwa yana damfarar maza (Hotuna)

Ana dai samun karuwar sace mutane da sauran muggan laifuka a jihar inda wasu ke shafar manyan mutane.

A makon da ta gabata, an sace wani Farfesa a Jami'ar Fasaha ta Moddibo Adama amma an sako shi bayan an biya kudin fansa na naira miliyan biyu a cewar iyalansa.

A cikin satin dai, an kashe shugaban kungiyar Fulani ta Tabbital Pulaku Jonde Jam, Alhaji Abdu Bali a gidansa da ya Yola, babban birnin jihar.

Da aka tuntube shi kan satar mutanen da aka yi a ranar Asabar, Kakakin 'yan sanda na jihar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar da lamarin inda ya kara da cewa mutum hudu aka sace.

Ya ce, "mutum hudu aka sace amma masu garkuwa da mutanen sun saki daya daga cikinsu domin ya zo gida ya isar da sakon."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel