Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya musanta ikirarin David Cameron

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya musanta ikirarin David Cameron

- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya musanta zargin da tsohon firayem ministan Birtaniya ya yi masa

- Jonathan ya bukaci jama'a da suyi watsi da maganganun tsohon firayem ministan don babu kamshin gaskiya

- Ya kara da cewa, ba shi ne na farko da ya gano karyar da ke cikin littafin ba, mutane da yawa sun gano

Tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan, ya musanta ikirarin tsohon firayem ministan Birtaniya, David Cameron.

David Cameron ya ce tsohon shugaban kasar ya ki karbar tayin rundunar sojin Birtaniyan don ceto 'yam matan Chibok da 'yan ta'addan Boko Haram suka yi garkuwa dasu.

A maida martanin da Jonathan ya yi a ranar asabar, ya bukaci jama'a da suyi watsi da zancen.

KU KARANTA: Da arziki a gidan wasu: An binciko wani tsohon gwamna da ya siyarwa kansa motocin gwamnati a rahusa

"Na karanta tsokacin tsohon firayem ministan Birtaniya, David Cameron, a sabon littafinsa, inda ya zargeni da gwamnatin Najeriya da nake shugabanta a lokacin da laifin rashawa da kuma kin karbar tayin gwamnatin Birtaniya wajen ceto 'yam matan Chibok wadanda aka sace a ranar 14 ga watan Afirilu, 2014," Jonathan ya rubuta a shafinsa na Facebook.

"Abin haushi ne da Cameron ya ce hakan, saboda abu makamancin hakan bai faru ba. A matsayin shugaban kasa na lokacin, ba David Cameron ba, har Barrack Obama na rubutawa wasika don neman tallafi wajen ceto 'yam matan,"

"Akan me zan bukaci taimako kuma in zo in ki taimakon daga baya?"

A lokacin na halasta turo rundunar sojin Amurka da Isra'ila don a ceto 'yam matan, toh akan me Cameron zai fadi haka babu kunya?

"Ina bukatar jama'a su yi watsi da ikirarin Cameron. Ban zama mutum na farko ba da ya zargesa da karya a wannan littafin. Idan kuma na duba martanin da ake ta maida mishi, ba zan zamo na karshe ba," ya kara.

Jonathan ya ce gwamnatin Theresa May, wacce ta gaji Cameron, ta taba bankado karairayin da aka yi a cikin littafin akan garkuwa da 'yam matan Chibok.

Ya ce Cameron bai zo da tallafi ba, shi ne ma ya bukaci tallafin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel