Yanzu-yanzu: Gwamnatin Ekiti za ta soma biyan N30,000 mafi karancin albashin a watan Oktoba

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Ekiti za ta soma biyan N30,000 mafi karancin albashin a watan Oktoba

Gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi ya ce gwamnatinsa za ta fara biyan naira 30,000 mafi karancin albashi daga wannan watan na Oktoba.

Fayemi ya ce kaddamar da sabon mafi karancin albashin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatinsa ke kokarin ganin ta faranta rayuwar ma’aikatanta musamman malaman makaranta.

KU KARANTA:Masari ya nada sabbin masu bada shawara na musamman 14 ga gwamnatinsa

Gwamnan yayi wannan furucin ne a filin wasanni na Oluyemi Kayode a wurin taron ranar malamai ta shekarar 2019, ranar Asabar 5 ga watan Oktoba, 2019.

A wurin taron an karrama wasu malamai uku, Mista Henry Olaoluwa Asubiojo na makarantar Amoye Grammar School, Tajudeen Olaoye na makarantar Anglican Primary School da kuma Misis Mojisola Ehinafe ta makarantar Technical School, Ado Ekiti inda aka ba ko wannensu N500,000 na kasancewarsu malamai mafiya hazaka a makarantunsu.

Fayemi ya ce yana nan da shirin bude sabbin makarantu a Ado Ekiti babban birnin jihar Ekiti domin rage cinkoson makarantun da suke cike makil da dalibai.

“Hanya guda daya ce kawai zamu iya bi domin dawo da martabar ilimi a jihar nan tamu kuma wannan hanyar ita ce, karfafawa malaman makarantar gwiwa.

“Zan bada himma wurin habbaka ilimin kimiyya da fasahar zamani a jihar nan. Kuma zan sanya ido sosai domin tabbatar da cewa duk yaron da ya isa shiga makaranta iyayensa sun tura shi. Saboda bayar da ilimi firamare da karamar sakandare wajibi a bisa dokar Najeriya.” Inji Fayemi.

Farfesa Isaac Adeoluwa, shugaban Kwalejin ilimi ta Ekiti, da yake gabatar da nasa jawabin a wurin taron ya ce, idan har Najeriya na son ganin ta samu cigaba mai amfani dole sai an inganta ayyukan malamai ta yadda za su rika tafiya da zamani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel