Masari ya nada sabbin masu bada shawara na musamman 14 ga gwamnatinsa

Masari ya nada sabbin masu bada shawara na musamman 14 ga gwamnatinsa

Gwamna jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana kudurinsa na yiwa ma’aikatun gwamnatin jihar kwaskwarima ta hanyar fito da sabbi da kuma rage wasu daga cikin wadanda suke a kasa yanzu haka.

Masari wanda ya fadi hakan a yayin da yake rantsar da masu ba gwamnatinsa shawara 14 ya ce, wannan matakin ya zama wajibi ne domin samar da majalisar zartarwa wadda za ta kawo cigaban da ake bukata a jihar Katsina.

KU KARANTA:Masu gudu su gudu: Majalisar wakilai za ta karawa EFCC da ICPC karfi saboda yaki da cin-hanci da rashawa

Wadanda aka rantsar a matsayin masu ba gwamnan shawara sun hada da: Bashir Dayyabu, Lawal Tanimu (Kwadago), Kabir Shuaibu (Lamuran siyasa) da Abdullahi Mahuta (lamuran majalisar dokoki).

Sauran kuwa su ne; Muntari Lawal, Bashir Ruwan Godiya, Abdulkadir Mamman Nasir, Hussaini Adamu Karaduwa, Khalil Ibrahim Lawal Jibiya, Lawal Usman Bagiwa, Hamza Muhammad Borodo, Dr Abba Abdullahi da kuma Abdu Habu Dankum.

Da yake jawabi jim kadan bayan rantsar da wadannan mutanen, Gwamnan ya tunatar da wadanda aka sake nadawa mukamin a karo na biyu, a matsayin nuna jajircewarsu ga taimakon gwamnatin.

Masari ya ce: “Wadanda kuma aka nada sabbi za su iya kasancewa sabbi a majalisar zartarwar wannan gwamnatin amma ba sabbi bane a cikin tafiyar jam’iyyarmu ta APC. Kamar da a ce an mayar da abu mazauninsa na asali.”

Ya kuma kara da yin kira a gare su na su kasance su na sanya bukatun jama’a a farko a duk lokacin da suka tashi aiwatar da wani aiki ko bayar da shawarwari.

Taron ya samu halartar mataimakin gwamnan jihar Katsina, Mannir Yakubu, kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Tasi’u Zango da dai sauran wasu manya-manyan mutanen jihar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel