Jiragen yakin NAF sun sake tarwatsa wani mabuyar 'yan ta'adda a Borno

Jiragen yakin NAF sun sake tarwatsa wani mabuyar 'yan ta'adda a Borno

Rundunar Sojojin Saman Najeriya (NAF) ta sake lalata wata mabuyar 'yan ta'addan kungiyar Islamic State of West Africa Province (ISWAP) da 'yan Boko Haram da ke jihar Borno.

Rundunar ta NAF ta kuma ni nasarar kashe mayakan kungiyar da dama a garin Kirta Wulgo da ke kusa da Tafkin Chadi a jihar.

Direktan yada labarai da bayyanai na NAF, Air Commodore Ibikunle Daramola ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a birnin tarayya Abuja.

Daramola ya ce sashen kai harin jiragen sama na Operation Lafiya Dole ne suka kai harin a ranar Juma'a kamar yadda The Nation ta ruwaito.

DUBA WANNAN: An kama wani gardi da ya yi basaja a matsayin karuwa yana damfarar maza (Hotuna)

Ya yi bayanin cewa an kai harin saman ne bayan samu wadansu bayanan sirri da suka tabbatar lallai mayakan na Boko Haram suna wurin kuma suna amfani da shi a matsayin sansanin da suke shiri idan za su kaiwa dakarun sojoji hari.

Ya ce, "Daga bisani sashin kai harin jiragen saman ta aike da jiragen yaki domin kai hari a wasu gidaje a kauyen.

"Kamar yadda aka gano, mayakan ISWAP da dama sun yi yunkurin tserewa da suka hango jirgin yakin na sojojin.

"Jiragen daya bayan daya sunyi seti sannan suka yi luguden wuta a dai-dai gidajen da 'yan ta'addan suke wadda hakan ya yi sanadiyar lalata gidajen tare da kashe 'yan ta'dda da dama."

Daramola ya kara da cewa NAF, tare da sauran dakarun sojoji na kasa za su cigaba da yakin da suke yi har sai sun ga bayan 'yan ta'addan da suka yi saura a yankin na Arewa maso Gabas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel