Masu gudu su gudu: Majalisar wakilai za ta karawa EFCC da ICPC karfi saboda yaki da cin-hanci da rashawa

Masu gudu su gudu: Majalisar wakilai za ta karawa EFCC da ICPC karfi saboda yaki da cin-hanci da rashawa

Majalisar wakilai a Najeriya ta bayyana kudurinta na ganin bayan cin-hanci da rashawa ta hanyar sake karfafa hukumomin EFCC da ICPC a kasar. Inda ta ce dokar da hukumomin ke aiki da ita a yanzu ta gaza wajen kawar da rashawa a Najeriya.

Majalisar wakilan ta ce dokar hukumomin yaki da cin-hancin a Najeriya sun gaza kwarai da gaske, hakan ne ma ya sanya har ila yau an kasa magance matsalar rashawa da cin-hanci da ta zama ruwan dare a kasar nan.

KU KARANTA:Mafi karancin albashi: Sabon rikici ya kunno kai game da maganar rage yawan ma’aikata da gwamnatin tarayya ta yi

An fitar da wannan kudurin ne a zaman majalisar na ranar Alhamis 3 ga watan Oktoba, inda aka cikinsa aka ambaci sabbin dokoki da tsare-tsare na musamman wadanda za a iya amfani da su domin magance matsalar cin-hanci a kasar nan.

Hon. Julius Ihonvbare ne ya karanto kudurin ga majalisar wanda bayan an tafka muhawara kudurin nasa ya samu amincewar akasarin mambobin majalisar wakilan.

Da yake nasa jawabin game da shekaru ashirin na siyasar dimokuradiyya a Najeriya, Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ya ce: “Wannan majalisar ta mu ta 9, bamu da wani abinda ke gabanmu da ya wuce kare bukatun mutanenmu.

“Kada ku manta jama’armu muke wakilta a wannan wurin da muke zaune, a don haka duk abinda zamu yi domin farin cikinsu ne. Ya zama wajibi mu rika jiyo ta bakinsu ire-ire matsalolin dake damunsu domin mu kawo su majalisa a sama masu mafita.

“Babban abinda ya sa al’umma ke yiwa dimokuradiyya wani irin kallon shi ne cin-hanci da rashawa, kawar da wannan abu shi ne burinmu a halin yanzu.” Inji Gbajabiamila.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel