Pantami da Abdullahi za su jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron GITEX a Dubai

Pantami da Abdullahi za su jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron GITEX a Dubai

Ministan Sadarwa na Najeriya, Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami FNCS, FBCS, FIIM, zai jagoranci tawagar manyan 'yan kasuwar Najeriya zuwa taron kimiyyar sadarwa ta 'Gulf Information Technology Exhibition' (GITEX 2019) da za ayi a Dubai daga ranar 6 zuwa 10 ga watan Okotoban 2019.

A cewar sanarwar ta shugaban sashin hulda da al'umma na NITDA, Hadiza Umar ta fitar a ranar Juma'a a Abuja, tawagar ta Najeriya za ta hadu da wasu 'yan kasuwan fiye da 200,000 daga kasashe fiye da 145 inda za su tattauna kan sabbin dabarun dake fanin sadarwa.

Ministan zai bayyana wa masu neman saka hannun jarin irin ribar da za su samu idan suka saka hannun jari a sashin na sadarwar (ICT) na Najeriya kamar yadda The Witness ta ruwaito.

DUBA WANNAN: An kama wani gardi da ya yi basaja a matsayin karuwa yana damfarar maza (Hotuna)

Pantami zai yi bayyani kan dalilan da suka sa a halin yanzu Najeriya ta zama kasuwar da masu hannun jari za su samu amfani sosai idan suka kawo kasuwancinsu duba da yadda gwamnati ta sauya kallubalen da kasar ke fuskanta suka zama alheri da kuma yadda tsare-tsaren gwamnati na saukaka kasuwanci zai amfane su musamman a fannin sadarwa.

Taron zai bawa masu neman saka hannun jari damar fahimtar alherin da ke kasar a fannin sadarwa musamman a fanin Ilimi, tsaro na intanet, makamashi, kiwon lafiya, kimiyyar noma, kafa masanantu da sauransu.

Ba boyayen abu bane cewa Najeriya ce kasuwa mafi girma a nahiyar Afirka duba da cewa tana kan gaba wurin tattalin arziki. Kasar bakar fata mafi yawan al'umma a duniya za ta nuna wa duniya irin alherin da za su samu idan suka saka hannun jari a kasar.

Za a tattauna muhimman batutuwa da suka shafi fanin na sadarwa a taron da za a kwashe kwanaki biyar ana gudanarwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel