Mafi karancin albashi: Sabon rikici ya kunno kai game da maganar rage yawan ma’aikata da gwamnatin tarayya ta yi

Mafi karancin albashi: Sabon rikici ya kunno kai game da maganar rage yawan ma’aikata da gwamnatin tarayya ta yi

Gamayyar kungiyar ‘yan kwadago ta yi watsi da batun ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige ya fadi na cewa gwamnatin tarayya na bukatar rage yawan ma’aiktan kafin ta samu damar kaddamar da mafi karancin albashin N30,000.

Sakataren kungiyar, Alade Lawal ne ya shaidawa jaridar The Nation cewa ko kadan wannan barazanar da gwamnati ke yi bata kama jikinsu ba.

KU KARANTA:Ba zan daga hannun ko wane dan takara ba a zaben 2023, inji wani gwamnan jihar arewa

Ya kuma yi korafin a kan maganar da Ngige yayi ta cewa gwamnati na bukatar kudin da yawansu ya kai N580bn a duk shekara domin biya ma’aikata mafi karancin albashin.

Lawal ya ce: “A iya sani na dai duk wanda ke maganar cewa za a rage yawan ma’aikata ta hanyar sallamar wasu yana bata bakinsa ne kawai. Ana yin hakan domin a hana cinma burin da muka sa a gaba na ganin gwamnati ta fara biyan sabon albashin.

Ya cigaba da cewa: “Ko kadan mu ba mu kallon wannan maganar, idan har sun shirya sai su zo mu zauna domin mu daddale magana guda daya. Ta yaya za a ce gwamnati ta gaza cinma matsaya game da bukatun kungiyar kwadago?

“Ka wai basu shirya yin abinda ya dace bane. Ba kuma naira biliyan 580 ake bukata kafin a fara biyan sabon albashin ba. Gaba daya ma’aikatan Najeriya ba su kai miliyan daya ba, idan kuwa har da gaske suke yi abu ne wanda bai fi karfinsu ba.” Inji Lawal.

Bugu da kari, Lawal ya ce har yanzu gwamnatin tarayya ta ki cewa komi game da bukatunsu game da yadda suke son a biya mafi karancin albashin ga ma’aikata.

https://thenationonlineng.net/minimum-wage-fg-workers-face-off-worsens-as-labour-rejects-sack-option/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel