Ba zan daga hannun ko wane dan takara ba a zaben 2023, inji wani gwamnan jihar arewa

Ba zan daga hannun ko wane dan takara ba a zaben 2023, inji wani gwamnan jihar arewa

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya ce ba zai daga hannun ko wane dan takara ba a matsayin wanda zai tsaya takarar kujeran gwamnan jihar a zaben 2023.

Ortom ya fadi wannan maganar ne ranar Juma’a 4 ga watan Oktoba, 2019 a Makurdi babban birnin jihar Benue yayin da yake zantawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a jihar.

KU KARANTA:Zaben Kogi: PDP ta nada kwamitin kamfe saboda zaben gwamnan jihar

Kamar yadda Gwamna Samuel ya fadi, zan bai wa jam’iyya damar zaben duk wanda take ganin ya dace da wannan kujera domin ta tsaida shi takarar gwamnan.

Gwamnan ya ce: “Idan wani ya zo ya ce maku ni na zabe shi a matsayin dan takarata ku ce masa karya yake yi, saboda ni duk wanda jam’iyya ta tsaida a zaben 2023 ina tare da shi.

“Kada wani ya zo domin ya yaudareku da sunan cewa dan takarata ne musamman a lokacin da zaben 2023 ke dada matsowa.”

Haka zalika, gwamnan ya bai wa jam’iyyar shawara kan cewa kada tayi watsi da tsarin karba-karba a lokacin da take kokarin fitar da wadanda za su tsaya takarar kananan hukumomi da kuma kansila a zaben 30 ga watan Nuwamba.

“Karba-karba ne kadai abinda zai iya samarwa jamiyyarmu nasara. Ina kira ga ‘yan takararmu da kada suyi amfani da son zuciyarsu domin sauya tsarin karba-karban in dai har nasarar PDP ke gabansu.” Inji Ortom.

A karshe Gwamnan ya sake jaddada kudurinsa na daga martabar jihar Benue fiye da yadda take a halin yanzu, inda ya ce ayyuka ma yanzu aka soma akwai saura na nan tafe.

https://www.vanguardngr.com/2019/10/ortom-ill-not-anoint-anybody-as-my-successor-2/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel