Zaben Kogi: PDP ta nada kwamitin kamfe saboda zaben gwamnan jihar

Zaben Kogi: PDP ta nada kwamitin kamfe saboda zaben gwamnan jihar

Jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP ta nada kwamitin yaki neman zabe wato kamfe saboda zaben gwamnan jihar Kogi wanda ke tafe a ranar 16 ga watan gobe.

Da yake magana a wurin taron nadin kwamitin, shugaban PDP a jihar Kogi, Mr Samuel Uhuotu ya roki mambobin kwamitin da su yi kamfe mai cike da manufa.

KU KARANTA:Babu dalilin da zai sa a raba Najeriya – Gbajabiamila

Haka kuma ya shawarcesu da su guji furta kalaman batanci ga ‘yan jam’iyyun adawa a yayin gudanar da yakin neman kuri’u.

Ubuntu ya ce, dan takarar PDP Musa Wada shi ne kan gaba a sahun wanda ake sa ran za su lashe zaben mai zuwa. Wannan kuwa bai rasa alaka da rashin nagartar gwamnati mai ci a yanzu, saboda haka cikin sauki zamu karbe kujerar gwamnan.

Tajudeen Yusuf shi ne Darakta janar an kwamitin yakin neman zaben Musa/Aro, kuma ya ce kwamitinsa ya riga da ya kammala shirye-shiryen soma yakin neman kuri’un ko wane lungu da sako na jihar Kogi.

Yusuf sake yin kira ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta shiri na musamman domin ayi zabe cikin lumana da zaman lafiya.

Sakataren hulda da jama’a na PDP a matakin kasa, Kola Ologbondiyan ya yi kira ga masu jefa kuri’a da suyi amfani da kuri’arsu ta hanyar da ta dace domin tsamo kansu daga cikin halin kangi da talauci.

Ya kuma bayyana farin cikinsa bisa tarin jama’ar da ya gani a wurin taron nadin kwamitin yakin neman zaben Musa/Aro. A nasa jawabin dan takarar gwamnan karkashin jam’iyyar PDP, Musa Wada ya yi kira ga jama’a da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin zaben PDP ranar 16 ga watan Nuwamba.

https://guardian.ng/news/pdp-inaugurates-campaign-committee-for-kogi-governorship-poll/amp/?utm_term=Autofeed&echobox=twitter_post&utm_medium=Social&utm_source=Twitter&__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel