Babu dalilin da zai sa a raba Najeriya – Gbajabiamila

Babu dalilin da zai sa a raba Najeriya – Gbajabiamila

-Kakakin majalisar wakilai ya ce babu wani dalilin da zai sa a raba Najeriya

-Femi Gbajabiamila ya fadi wannan maganar ne a lokacin da yake karbar bakuncin kungiyar Arewa Youth Forum a ofishinsa dake Abuja

-Shuwagabanni da suka gabata sun yiwa kasar nan kokari yanzu lokaci ne na matasa, a cewar Femi

Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ya ce Najeriya za ta cigaba da kasancewa a matsayin kasa guda daya tal duk wuya duk runtsi.

Gbajabiamila ya ce ‘yan Najeriya na da dalilai masu tarin yawa da ya kamata su kasance tare cikin hadin kai da kaunar juna domin cigaban kasar.

KU KARANTA:Ka rage albashin sanatoci da 'yan majalisr wakilai domin samawa 'yan Najeriya aikin yi, sakon Sarki Sanusi zuwa ga Buhari

Kakakin majalisar wakilan yayi wannan maganar ne a lokacin da wata kungiyar matasan arewa ta kawo masa ziyara a ofishinsa dake Abuja, inda ya ce shuwagabannin da suka gabata sun yi iya bakin kokarinsa game da kasar nan, a don haka yanzu lokacin matasa ne.

Har ila yau, Gbajabiamila ya ce majalisar dokokin a shirye take domin karbar shawarwari daga kungiyoyi musamman na matasa wadanda kan iya zama sanadiyar samun cigaba a Najeriya.

Da yake magana a kan irin muhimmanci da majalisarsa ke bai wa matasa, Femi ya ce: “Majalisar dokoki ba komi take da buri ba in banda hadin kan ‘yan Najeriya. Kasar nan kasa guda ce abinda masu iya magana ke cewa ‘tsintsiya madaurinki guda’.

“Akwai masu kace nace da kuma hana ruwa gudu a gefe, a don haka kada ku fasa kuma ina kira a gareku da ku rika yin biris da irin wadannan maganganun idan kun ji su. Akwai hikima mai tarin yawa cikin hadamu waje guda da Allah yayi.” Inji Kakakin.

A cikin bayanin shugaban kungiyar, Gambo Ibrahim Gujungu, wanda shi ne ke jagorantar jihohin arewa 19 ya godewa kakakin bisa kayan tallafin da ya rabawa sansanin ‘yan gudun hijira a jihohin Borno, Katsina da Zamfara.

https://leadership.ng/2019/10/05/nigeria-will-remain-indivisible-gbajabiamila/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel