'Yan bindiga sun kashe sojoji 9 a jihar Zamfara

'Yan bindiga sun kashe sojoji 9 a jihar Zamfara

- A ranar Alhamis cikin dare ne 'yan ta'adda a kauyen Sunke, karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara suka aukawa sojoji

- 'Yan ta'addan sun kashe sojojin ne don maida martanin kashe tubabbu da sojojin suka yi

- Harin ya biyo bayan sanarwar da gwamnatin jihar ta yi na cewa akwai yuwuwar harin 'yan ta'addan Boko Haram a kananan hukumomi 7 na jihar

A ranar Alhamis cikin dare ne 'yan bindiga suka kashe sojoji 9 a kauyen Sunke da ke karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Rahoton ya nuna cewa, 'yan bindiga masu yawa sun je kauyen Sunke a babura inda suka dinga harbin sojoji da 'yan sanda.

KU KARANTA: Allah mai iko: Tayi nakuda har ta haihu a karkashin gada

Majiya daga gwamnatin jihar, ta sanar da jaridar Daily Trust cewa harin da 'yan bindigar suka kai, maida martani ne ga kisan 'yan ta'addan da sojoji suka yi.

Majiyar ta ce, "Sojoji sun kashe wasu 'yan ta'adda da suka tuba kuma sunyi alkawarin maida martani. Tubabbun 'yan ta'addan sun turo 'yan uwansu inda suka afkawa sojoji a kauyen,"

A ranar Laraba, mazauna yankin sun ga 'yan bindiga akan babura inda suka bi babban titin Gusau zuwa Sokoto. 'Yan bindigar sunce suna tafiya ne zuwa Birnin Gwarin jihar Kaduna.

Harin ya biyo bayan kusan sati biyu da gwamnatin jihar ta sanar da cewa akwai yuwuwar harin 'yan Boko Haram a kananan hukumomi 7 na jihar.

Mai magana da yawun rundunar 'Operation Hadarin Daji' na jihar, Captain Oni Orisan ya yi alkawarin kara tattaunawa akan lamarin da wakilin Daily Trust.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel