Tsananin talauci ya sanya saurayi tono gawar mahaifinsa da ya mutu shekaru 14 da suka wuce, domin ya cire kayan da aka binne shi da su

Tsananin talauci ya sanya saurayi tono gawar mahaifinsa da ya mutu shekaru 14 da suka wuce, domin ya cire kayan da aka binne shi da su

- Tsananin talauci ya sanya wani saurayi ya tono gawar mahaifinsa domin ya cire kayan jikinsa ya sayar

- Bayan tono gawar ya tarar da kayan duk sun rube, domin kuwa mahaifin nasa ya shekara 14 da mutuwa

- Wannan abu dai ya faru a kasar Kenya ne, inda 'yan sanda suka yi gaggawar cafke saurayin

An kama wani saurayi dan kasar Kenya yana tono gawar mahaifinsa saboda ya cire wani takalmin fata da aka binne shi da shi.

Mutumin dan shekara27 mai suna Patrick Mwangi Katonye an kama shi da safiyar Allah misalin karfe 8 na safiyar ranar Larabar nan da ta gabata, a kauyen Maseno.

A cewar shugaban rundunar 'yan sandan Nakuru, Stephen Matu, saurayin yana kokarin tono wani takalmin fata da aka binne mahaifinsa Johnson Ndonye a lokacin da ya rasu a shekarar 2005. Shugaban rundunar 'yan sanda ya bayyana cewa saurayin yana so ya sayar da takalmin ne.

"Wanda ake zargin ya bayyana mana cewa yana so ya sayar da takalmin ne, hakan ya saka ya jira sai da duka 'yan gidan suka fice sai ya fara tono takalman, amma kuma bayan ya tono sai ya tarar takalmin ya rube," in ji Matu.

KU KARANTA: Jaruma Fati Washa ta sha tofin Allah tsine a wajen masoyanta bayan ta wallafa wani hotonta na tsiraici

'Yan sandan dai sun kama saurayin inda suka nufi asibitin mahaukata da shi, kafin daga baya a kai shi kotu domin yi masa hukunci akan abinda yayi.

Matu ya bayyana cewa 'yan uwan mamacin sun bukaci a kyalesu su kara yi masa addu'a kafin a mayar dashi a binne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel