Wata budurwa ta sayar da jaririnta, saboda ta samawa saurayinta kudin da zai fita kasar waje

Wata budurwa ta sayar da jaririnta, saboda ta samawa saurayinta kudin da zai fita kasar waje

- Wata budurwa a kasar Ghana ta sayar da dansu guda daya tilo da suka haifa da saurayinta

- Budurwar ta sayar da dan nasu ne mai watanni uku kacal a duniya domin ta samawa saurayin nata kudin da zai tafi kasar waje

- Wannan abu bai yiwa saurayin dadi ba domin kuwa cikin gaggawa ya kai karar ta wajen hukumar 'yan sanda

Jami'an hukumar 'yan sandan kasar Ghana sun kama wata budurwa mai shekaru 25 da aka bayyana sunanta da Sarah Kwabla, da laifin sayar da jaririnta mai watanni uku kacal, domin ta samawa saurayinta mai suna Akwasi Botwe kudin da zai samu ya tafi kasar waje.

Abokin Akwasi Botwe wanda yake zaune a kasar Faransa, yayi mishi alkawarin zai iya kai shi kasar Faransa idan har ya samu ya tara cedi dubu goma (Ghc10,000) kimanin naira dubu sittin da bakwai (N67,000) kenan a kudin Najeriya, sai dai kuma shi iya Ghc2,000 kawai ya iya samu ya tara saboda ba shi da aikin yi.

KU KARANTA: Jaruma Fati Washa ta sha tofin Allah tsine a wajen masoyanta bayan ta wallafa wani hotonta na tsiraici

Sai dai kuma yayi mamaki matuka, inda ya dinga yiwa kanshi tambayoyi bayan budurwar shi ta turo masa guntun cikon kudin cikin asusun shi a ranar 24 ga watan Satumba.

Da ya tambayeta yadda aka yi ta samo kudin, sai take gaya masa cewa ta sayar da dansu ne da suka haifa tare mai watanni uku a duniya.

Daga baya 'yan sanda sun kama Sarah, bayan saurayin nata ya kai karar ta wajen hukumar 'yan sanda. Har yanzu dai 'yan sandan na can suna gabatar da bincike akan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel