Allah ya kyauta: An kama wata mata da taje za ta jefa 'ya'yanta guda biyu a cikin rijiya

Allah ya kyauta: An kama wata mata da taje za ta jefa 'ya'yanta guda biyu a cikin rijiya

- Har zuwa yanzu dai hukuma ta kasa kawo karshen dalilan da ya sanya iyaye ke zama barazana ga 'ya'yansu

- Yayin da zaka iske a lokuta da dama, uba ya yiwa 'yarsa ta cikinsa fyade ko kuma wani abu makamancin haka

- A wannan karon dai wata mata ce aka kama ta a lokacin da ta dauki 'ya'yanta guda biyu ta nufi rijiya za ta tsunduma su a ciki

Wani bidiyo da yake ta faman yawo a kafafen sadarwa ya bayyana yadda aka kama wata mata a lokacin da take kokarin jefa 'ya'yanta guda biyu cikin rijiya.

Da aka tambayeta dalilin da yasa za ta jefa 'ya'yan nata, matar tayi shiru taki yin magana, ta koma tamkar kurma.

Daga baya dai an mikawa jami'an hukumar 'yan sanda matar domin yin bincike a kanta, saboda mutane na ganin cewa kamar ta samu tabin hankali ne.

KU KARANTA: Kwamacala: Budurwa ta auri samari guda biyar rigis duka 'yan uwan juna a lokaci daya

An ruwaito cewa wannan lamari dai ya faru ne a ranar 3 ga watan Oktobar 2019 dinnan, a kan layin Kushimo dake yankin Ikotun Egbe dake cikin jihar Legas.

A lokuta da dama akan samu irin wannan abu yana faruwa a Najeriya, yayin da iyaye za su dinga kokarin kashe 'ya'yansu da hannunsu.

Haka zalika mun kawo muku rahoton yadda wata budurwa a kasar Indiya ta auri maza guda biyar 'yan gida daya a lokaci daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel