'Dan yi wa kasa hidima ya yi amfani da basirarsa ya kera wa dalibansa kujeru (Hotuna)

'Dan yi wa kasa hidima ya yi amfani da basirarsa ya kera wa dalibansa kujeru (Hotuna)

- Wani matashi dan yi wa kasa hidima, Stephen Teru ya bayyana irin aikin taimako da ya yi wa mutanen garin da ya tafi yin hidima

- Stephen wadda dama kafinta ne ya yi amfani da basirarsa wurin kera kujeru da fiye da dalibai 80 ke amfani da shi a makarantu

- Matashin ya kuma mika godiyarsa da al'ummar garin da iyalansa

Karamci da kirki hali ne da ba mutane da yawa ke da shi ba a halin yanzu. Wasu kuma na ganin sai masu arziki ne kadai za su iya tausayawa na kasa da su. Sai dai ba haka zancen ya ke a kowanne lokaci ba domin akwai mutanen da ke kokarin tsayuwa da kansu amma su kan tallafawa wasu a rayuwa.

Legit.ng ta tattaro rahoton wani dan yi wa kasa hidima, Stephen teru wadda ya yi amfani da basirarsa a matsayin kafinta ya kera kujeru da dalibai fiye da 80 ke amfani da shi a makarantu a garin da ya ke hidima.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan Boko Haram suna can suna kone gidajen al'umma a Chibok

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce wannan gudunmawarsa ne ga makarantun biyu da ke garin da ya ke hidima wato Community Secondary School da St. Georges Primary School.

Matashin ya kuma nuna hotunnan ayyukansa da ya yi inda ya mika godiya ga mutanen garin da iyalansa.

Ga hotunan a kasa:

Tubarkalla!

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel