Sifeta janar na 'yan sanda ya raba babura da Keke Napep ga 'yan sanda

Sifeta janar na 'yan sanda ya raba babura da Keke Napep ga 'yan sanda

- IG na rundunar 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya rabawa 'yan sandan Kano da Jigawa da Katsina babura da Keke Napep

- An bawa jami'an 'yan sandan baburan da Keke Napep din ne kan bashi na kudi N283,000 ne Keke da N735,000

- Sufeta Janar din ya ce an bawa jami'an 'yan sandan wannan tallafin ne domin inganta walwalarsu da ta iyalansu

Akalla jami'an 'yan na yanki na farko da suka kunshi jihohin Kano, Jigawa da Katsina 1,000 ne suka samu babura da Keke Napep da sifeta janar din 'yan sanda, Mohammed Adamu ya raba.

Sifeta janar din tare da hadin guiwar kungiyar hadin kan 'yan sandan yankin na farko ne suka raba baburan masu kirar Bajaj da Keke Napep din a ranar Juma'a.

Kungiyar ta sanar da jaridar Daily Trust cewa, burinta shi ne tabbatar da walwalar jami'an tsaron ta hanyar magance kalubalen rashin ababen hawa da suka fama da ita.

Yayin mika makullan ababen hawan ga jami'an da suka samu, mataimakin sifeta janar din yanki na daya, Dan Bature, ya hori jami'an da su maida alherin da aka musu ta hanyar jajircewa ga aiyukansu kamar yadda ya dace.

KU KARANTA: Ashshaa: Fasto ya umarci mazaje a coci da su saki matansu

"Jami'an 'yan sanda na aiki ba dare ba rana. Ganin haka ne yasa sifeta janar din ya kawo hanyar yalwata walwalar jami'an. Wannan an yi shi ne don karfafa musu guiwa ta yadda zasu bautawa Najeriya,"

"Ta wannan kungiyar hadin kan, jami'an sun samu gidaje da zasu dinga biya a hankali," Ya kara da.

Ya bayyana cewa, wannan shirin ya tabo duk yankuna 12 na 'yan sandan da ke fadin kasar nan.

Sakataren kungiyar kuma kwamishinan 'yan sanda, Dasuki D. Galadanci ya ce bashin an kara kashi biyar kacal ne akai kuma za a iya biya cikin shekara daya da rabi.

Ya bayyana cewa, babur N283,000 ne inda Keke Napeo ke N735,000.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Ahmed Iliyasu ya mika godiyarsa ga sifeta janar din tare da cewa ababen hawan zasu taimaka ba kadan ba a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel