'Yan bindiga sun kashe sojoji 9 a kauyen Zamfara

'Yan bindiga sun kashe sojoji 9 a kauyen Zamfara

Wasu da ke zargin 'yan bindiga ne sun kashe sojoji tara a kauyen Sunke da ke karamar hukumar Anka na jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce wasu 'yan bindigan da ba a san ko su wanene ba sun iso kauyen a kan babura inda suka rika bude wa sojoji da 'yan sandan da ke garin wuta.

The Nation ta ruwaito cewa wata majiya a gwamnatin jijar ta ce harin ramuwar gayya ne kan kisar sojoji suka yi wa wasu 'yan bindiga da suka tuba a baya-bayan nan.

"Sojoji sun kashe wasu 'yan bindiga da suka tuba kuma 'yan bindigan sun ce sai sun dauki fansa. Tubabbun 'yan bindigan sun tattaro 'yan uwansu sun kaiwa sojoji farmaki a kauyen," a cewar majiyar.

DUBA WANNAN: Gwamnan PDP ya umarci a mayar da sunan Sardauna a titin da aka sauya da sunansa

A ranar Laraba da ta gabata, mazauna kauyen sun hangi tawagar 'yan bindiga a kan babur a mahadar Mayanchi kan babban titin Gusau zuwa Sokoto.

'Yan bindigan sun ce suna hanyarsu ta zuwa garin Birnin Gwari ne a jihar Kaduna.

Harin na zuwa ne kusan makonni biyu bayan gwamnatin jihar ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne za su kai hari a wasu kananan hukumomi bakwai a jihar.

Da aka tuntube shi domin neman neman karin bayani a kan lamarin, kakakin Operation Hadarin Daji na jihar, Kyaptin Oni Orisan ya ce: "Ku bani lokaci zan neme ku. Sai dai bai amsa kirar wayar da aka yi masa ba a lokacin hada wannan rahoton."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel