Barayin da suka sace daliban Kaduna sun fadi kudin da za a biyasu kan su saki daliban

Barayin da suka sace daliban Kaduna sun fadi kudin da za a biyasu kan su saki daliban

Barayin da suka sace dalibai mata shida na Kwalejin Engravers dake Kakau Daji a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna sun ce sai an biya su miliyan N50 kafin su saki daliban da malamansu.

A safiyar ranar Alhamis 3 ga watan Oktoba ne wasu ‘yan bindiga suka shiga kwalejin suka yi awon gaba da dalibai mata shida tare da malamai biyu inda suka kai su wurin da ba a san ko ina ba ne har yanzu.

KU KARANTA:Rufe gidajen sayar da motoci: Hukumar kwastam ta gargadi dillalan cewa ka da su dauki doka a hannunsu

Jami’i mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ya tabbatar mana da aukuwar wannan lamari.

A lokacin da wakilin jaridar The Nation ya ziyarci makarantar wadda ke kauyen Kakau Daji inda daya daga cikin iyayen daliban da aka sacen ke sanar da shi cewa, barayin sun nemi hukumar makarantar ta biyasu naira miliyan 50 kan su sako daliban da malamai biyu.

Kamar yadda ya fada mana, daya daga cikin iyayen ya ce: “Mun samu labarin cewa barayin sun tuntubi hukumar kwalejin inda da farin suka bukaci a biya miliyan N30 kudin ko wane mutum guda.

“Abinda makarantar ta fada masu shi ne naira 100,000 kawai za ta iya biya domin a sako mata daliban da malamansu guda biyu. Barayin cewa suka yi baku shirya karbar dalibanku, idan kun shirya sai ku kira mu.”

Haka zalika, makarantar ta bayar da hutun kar-ta- kwana saboda sace dalibai mata shida da malamai biyu da akayi a makarantar don gudun faruwar wani mugun abu.

https://thenationonlineng.net/abductors-of-kaduna-school-girls-teachers-demand-n50m-ransom/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel