Abin Mamaki: Alkali ya harbe kansa ana tsaka da shari'a

Abin Mamaki: Alkali ya harbe kansa ana tsaka da shari'a

- Abin mamaki ya faru a wata kotu da ke yankin kudancin kasar Thailand

- Ana zaman kotu alkalin ya tashi tare da juyawa kotun baya, ya fito da karamar bindigarsa ya harbi kansa a kirji

- Tuni aka kwashesa rai a hannun Allah aka garzaya da shi asibiti don samun taimakon likitoci

A ranar juma'a ne wani babban mai shari'a a yankin kudancin kasar Thailand yayin da yake cikin kotu ya tashi tare da harbin kansa a kirji.

Khanakorn Phianchana, babban alkali ne a kotun da ke yankin Yala a kasar Thailand.

Ya harbe kansa ne cikin kotu da bindigarsa inda aka kwashe shi zuwa asibiti.

KU KARANTA: Ashshaa: Fasto ya umarci mazaje a coci da su saki matansu

Bayan zartar da shari'a akan wani karamin batu, mai shari'ar ta sanar da mutanen da ke kotun cewa ya bani da rayuwar cike da aiyukan.

Jim kadan ya tashi tsaye tare da juya baya. Da sauri ya jawo karamar bindigarsa daga cikin riga inda a take ya harbe kansa.

Mai magana da yawun kotun, Suriyan Hongvilai, ya ce Khanakorn dama ya saba aiki mai tsananin wuya.

A halin yanzu dai majiya ta sanar cewa yana nan lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel