Yanzu-yanzu: 'Yan Boko Haram suna can suna kone gidajen al'umma a Chibok

Yanzu-yanzu: 'Yan Boko Haram suna can suna kone gidajen al'umma a Chibok

'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun can suna kone gidajen al'umma a kauyen Mifa da ke karamar hukumar Chibok na jihar Borno.

Wani mazaunin kauyen ya shaidawa The Cable cewa 'yan ta'addan sun shigo kauyen misalin karfe 8 na dare kuma nan take suka fara bankawa gidajen al'umma wuta.

"Suna kone gidaje a halin yanzu da muke magana da kai, sun zo da yawa a kan babura sun fara kone-kone," a cewar majiyar.

Ya ce mazauna kauyen da dama suna tserewa kuma harin ya razana al'umma a dukkan garin Chibok da kananan hukumomin da ke makwabtaka da Chibok.

DUBA WANNAN: Shugaba Halimah na cikin musulmi 50 da suka fi kowa karfin fada a ji a duniya

"Sun kone gidaje masu yawa saboda dare ne da kuma yanayin hanyar zuwa kauyen," inji shi.

"Ba mu san ko akwai wadanda suka mutu ba. Yanzunan sojoji suka iso duk da cewa 'yan ta'addan har yanzu suna cikin kauyen."

Mifa da ke nisan kilomita 8 daga Chibok shine kauye ne karshe da ke da iyaka da dajin Sambisa.

Wannan harin yana zuwa ne bayan ikirarin da hukumomin kasar suka ce sun ci galaba kan 'yan kungiyar Boko Haram.

A makonni kadan da suka shude, Shugaba Muhammadu Buhari ya sake jadada cewa an ci galaba kan 'yan ta'addan duk da cewa ya ce akwai kadan da su kayi saura.

Duk da cewa sojoji sun ce 'yan Boko Haram sune gudu don tsira da rayuwansu, an kuma ce 'yan ta'addan sun sayo sabbin makamai ciki har da jiragen yaki mara mataki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel