Satar dalibai: 'Dana zai cigaba da kasancewa a makarantar gwamnati – El-Rufai

Satar dalibai: 'Dana zai cigaba da kasancewa a makarantar gwamnati – El-Rufai

Gwamna Nasiru El-Rufa’i na jihar Kaduna yace dansa za cigaba da kasance a makarantar gwamnati duk da rahoton mamaye jihar da masu garkuwa da mutane da yan Boko Haram suka yi.

El-Rufa’i ya bayyana hakan ne yayinda yake martani da sace dalibai shida da malamai biyu da akayi a makarantar Engrave’s College a yankin Kakau Daji na jihar Kaduna a ranar Laraba.

Gwamnan, wanda yayi Magana da manema labarai na fadar Shugaban kasa a Abuja a ranar Juma’a, 4 ga watan Oktoba, yace kada dansa ya samu kariya fiyye da kowani da a jihar.

“Kada dana ya fi samun kariya sama da kowani da a jihar Kaduna.

“Na dauki rantsuwar aiki don kare kowa sannan dana mutum daya ne kawai cikin yara miliyan biyu da muke dasu a makarantun Firamare na jihar Kaduna sannan bani da kudirin sake duba hakan.

KU KARANTA KUMA: Malamai 4,692 za su rubuta jarabawar TRCN a Kaduna

“A gareni, kai dana makaranta gwamnati ba wai jaircewa da nayi bane kawai, sai dai nuni ga cewa na yarda da ingancin makarantun gwamnatinmu da har dana ya halarta.

“Mun rigada mun bayar da umurcin cewa ya zama dole dukkanin ma’aikatan da ke ma’aikatar ilimi su kasance yayansu na halartan makarantun gwamnati,” inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel