Garkuwa da mutane: Ba zan cire 'da na daga makarantar gwamnati ba - El-Rufa'i

Garkuwa da mutane: Ba zan cire 'da na daga makarantar gwamnati ba - El-Rufa'i

Gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna ya bayyana cewa ba zai cire yaronsa, Abubakar El-Rufa'i, daga makarantar gwamnati ba duk da garkuwa da mutanen da akayi da daliban wata makaranta a jihar jiya.

El-Rufa'i ya bayyana hakan ne yayinda yake tsokaci kan garkuwa da daliban makaranta 6 da malamai 2 a makarantar Engrave dake Kakau Daji a ranar Laraba.

Gwamna, wanda yayi jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa a Abuja ranar Juma'a ya ce yaronsa bai fi sauran yaran al'ummar jihar Kaduna ba.

Yace: "Bai kamata a ce yarona yafi sauran yaran Kaduna samun tsaro ba. Na yi rantsuwan kare rayukan kowa da kowa. 'Da na daya ne kawai daga cikin yara milyan biyu dake makarantun Kaduna kuma bani da niyya canza ra'ayi na."

"A kan al'amarin kai yarona makarantan gwamnati kuma, wannan alkawari ne na cika kuma hakan ya bayyana cewa na yi imani da ingancin makarantun gwamnati tun da yarona na zuwa."

Akan wadanda aka sace kuwa, gwamnan ya ce gwamnatin jihar, iyayen yaran da jami'an tsaro na iyakan kokarinsu wajen ganin ganin cewa an cetosu.

Gwamnan ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyayen yaran domin karban kudin fansa.

El-Rufa'i ya yi watsi da maganar cewa iyaye na cire yaransu daga makarantu saboda garkuwa da dalibai da akayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel