Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira babbar filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja da yammacin Juma'a, 4 ga watan Oktoba, 2019 bayan kwashe kwanaki biyu a kasar Afrika ta kudu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugaban kasar Afrika ta kudu, Cyril Ramaphosa, a ziyarar da ya kai kasar domin tattaunawa da takwararsa kan kisan yan Najeriya da wasu bakaken fata a kasar.

A jawabinsa, Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hare-haren da ake kaiwa yan Najeriya da wasu kasashen Afrika a kasar Afrika ta kudu, ya yi kira da gwamnatin kasar ta aiwatar da matakan da aka zayyana domin kiyaye gaba.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara kasar Afrika ta kudu a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, 2019 kan al'amarin kin jin bakin fata da ke addabi kasar Afrika ta kudu a makonnin bayan.

Shugaba Buhari zai tafi tare da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano, gwamna Simon Lalong na Plateau da gwamna David Umahi na Ebonyi.

Daga cikin ministoci akwai ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama; ministan tsaro, Bashir Magashi; ministan lantarki, Saleh Mamman; ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola; da ministan ma'adinai, Olamilekan Adegbite.

Sauran ministocin sune ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi da karamar ministar masana'antu, kasuwanci da hannun jari, Mariam Katagum.

Hakazalika akwai NSA Babagana Munguno, dirakta janar na hukumar NIA, Ahmed Rufai da shugabar hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel