Rikicin Boko Haram: Mutane sun gudu gaba daya a karamar hukumar Marte - Shettima

Rikicin Boko Haram: Mutane sun gudu gaba daya a karamar hukumar Marte - Shettima

Mutane sun arce gaba daya daga karamar hukumar Marte dake Arewacin jihar Borno , shugaban karamar hukumar, Alhaji Ali Shettima, ya laburta hakan.

Yayinda yake magana da manema labarai a Maiduguri, Alhaji Shettima ya bayyana cewa mutanen garin sun gudu daga muhallansu ne sakamakon hare-haren Boko Haram da yaki ci, yaki cinyewa.

Ya ce sun bar gudajensu zuwa sansanin yan gudun hijra dake wasu sassan jihar irin su Maiduguri da Monguno.

Shettima, wanda yayi Allah wadai da halin da al'ummarsa ke ciki ya ce "yawancin al'ummata za su so su kasance a gida yanzu duk da rikicin Boko Haram idan Sojoji suka basu dama."

KU KARANTA: Matashi ya yi garkuwa da kanwarsa, ya bukaci mahaifinsa N10m kudin fansa

A cewarsa: "An kauracewa karamar hukumar Marte gaba daya, ba za kaga mutum ko daya a Marte ba. Yawancin mutanen suna sansanin gudun hijra a Maiduguri.

"Kimanin iyalai 70,000 sune Monguno, muna da wasu a Gajiram kuma sauran na Gamboru. Yawancin iyalai sun rarrabu kuma babban kalubalen yanzu shine hada mutane da iyalansu."

"Sakamakon wannan rikicin, yawancin manoma sun gaza shiga gona. Kawai sun dogara da kudin hannun wasu domin rayuwa."

Shi kanshi a matsayin shugaban karamar hukumar ya gaza zama a cikinta, ya koma Maiduguri inda daga can yake gudanar da ayyukansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel