Tashin hankali: Matashi ya yi garkuwa da kanwarsa, ya bukaci mahaifinsa N10m kudin fansa

Tashin hankali: Matashi ya yi garkuwa da kanwarsa, ya bukaci mahaifinsa N10m kudin fansa

Wani matashi dan shekara 22, AbdulBasit Umar, ya shiga hannun hukumar yan sandan jihar Taraba sakamakon hada baki da abokansa wajen garkuwa da kanwarsa yar shekara 10 yayinda zata tafi makaranta.

AbdulBasit Umar, tare da abokansa biyu, Sadiq Sani da Abdullahi Habib, sun bukaci mahaifinsa kudi milyan goma matsayin fansa kafin su sake ta.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP David MIsal, wanda ya bayyanasu ga manema labarai tare da wasu mutane 12 da ake zargi da garkuwa da mutane sun yi bayanin cewa jami'an tsaro sun damkesu ne yayinda suka tafi amsan kudi N4million da aka yarje daga baya.

AbdulBasit Umar, wanda yayi ga manema labarai ya bayyana cewa bai taba aikata irin wannan abu ba amma ya bukaci kudin ne saboda yana son fita kasar waje karatu.

KU KARANTA: Rikicin Boko Haram: Mutane sun gudu gaba daya a karamar hukumar Marte - Shettima

A cewarsa, "Manufata itace idan na amsa kudin, zan tafi karatu kasar waje."

Daya daga cikin abokansa da suka aikata laifin, Sadiq Sani, ya ce kawai shi ya taya abokansa ne domin karban kudi daga hannun mahaifinsa.

A wani labarin mai kama da haka, Hukumar yan sandan jihar Gombe ta damke wani matashi dan shekara 19, Mohammed Sani Adamu, mazaunin Gabukka quaters kan zargin garkuwa da wani yaro mai shekaru 7 da haihuwa.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Obed Maru Malum, ta bayyanawa manema labarai cewa jami'an SARS sun damke matashin ne a ranar 23 ga Satumba, kwanaki uku bayan ya sace yaron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel