Rufe gidajen sayar da motoci: Hukumar kwastam ta gargadi dillalan cewa ka da su dauki doka a hannunsu

Rufe gidajen sayar da motoci: Hukumar kwastam ta gargadi dillalan cewa ka da su dauki doka a hannunsu

Hukumar hana fasa kwauri ta kwastam ta yi kira ga dillalan motoci cewa su kwantar da hankalinsu a game da garkame gidajen motoci a jihar Kaduna da wadansu jihohin dake makwabtaka da ita.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kwastam, Mr Joseph Attah ne ya fitar da wannan jawabin ranar Laraba 3 ga watan Oktoba, 2019 a Kaduna jim kadan bayan hukumar ta kammala ganawa da kungiyar manoman shinkafa na Najeriya.

KU KARANTA:Bamu bukatar Obaseki ya sake maimaita wa’adi na biyu – Kungiyar APC ta Edo

Attah ya sake gargadin dillalan inda ya ce, kada suyi gaggawar daukan doka a hannunsu saboda abinda hukumar ke yi yanzu zai iya zama mai amfani garesu a nan gaba. “Na san cewa mutane da dama cikinku sun samu labarin kwastam ta garkame gidajen motoci a jihohin Legas, Kano da sauransu a kwanakin baya.

“Sako kuwa a nan shi ne kada wani mai gidan mota ya ce zai dauki doka a hannunsa. Kowa ya kwantar da hankalinsa ya kuma cigaba da bin doka da oda, nan bada jimawa ba zamu fitar da jawabi na musamman game da abinda hukumarmu ta zartar.” Inji Attah.

Rahotanni da muka samu daga Daily Trust sun bayyana mana cewa, an samu wani halin rudani a tsakanin masu dillancin motoci a Kaduna sakamakon garkame gidajen sayar da motocin da hukumar kwastam ta yi a jihar.

https://www.dailytrust.com.ng/customs-calls-for-calm-over-car-dealer-offices-raid.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel