Ashshaa: Fasto ya umarci mazaje a coci da su saki matansu

Ashshaa: Fasto ya umarci mazaje a coci da su saki matansu

- Wani fasto a wat majami'a da ke kasar Zimbabwe ya baiwa mabiyansa shawarar sakin matansu

- Faston ya bada shawarar ne sakamakon rashin zuwan matan mabiyan nasa bauta

- Chipato ya dinga huduba kala-kala ga mabiyan nasa akan rashin amfanin zama da matan da basu zuwa majami'a

Wani fasto mai suna Philip Chipato ya umarci mabiyansa da su saki matansu da suka ki zuwa majami'a.

Kamar yadda B-Metro ta ruwaito, Chipato wanda majami'arsa ke arewacin Mahatshula da ke Bulawayo a kasar Zimbabwe ya umarci mazan da suka halarci cocin da su saki matansu da basu halarta ba.

KU KARANTA: Kotu ta yankewa wani tsohon babban sakataren tarayya shekaru 5 a gidan maza

Wani Fasto, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce Chipato ya dinga huduba tare da kushe matan aure da suka daina zuwa cocin.

Daga baya an gano cewa, Chipato ya umarci daya daga cikin fastocinsa mai suna Midzi, da ya saki matarsa Vimbai, wacce ta dena zuwa coci.

Majiyar ta ce, "Vimbai ta dena zuwa coci. Bayan kusan makonni biyu, Chipato ya fara darussa daya bayan daya akan ma'auratan da basu zuwa majami'a. A don haka ne ya bada shawarar su saki matan."

Duk da Chipato ya musanta bada wannan shawarar, majiyar daga cocin ta ce da yawa daga cikin masu zuwa cocin sun tsere saboda hudubar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel