Bamu bukatar Obaseki ya sake maimaita wa’adi na biyu – Kungiyar APC ta Edo

Bamu bukatar Obaseki ya sake maimaita wa’adi na biyu – Kungiyar APC ta Edo

Shuwagabannin jam’iyyar APC a karkashin Edo Peoples Movement (EPM) a ranar Alhamis 3 ga watan Oktoba, ta shaidawa Gwamna Godwin Obaseki cewar ba ta bukatar shi ya sake maimaita wani wa’adin mulkin a zaben gwamnan jihar da za ayi shekara mai zuwa.

Kungiyar ta ce za ta fita neman wanda ya fi Obaseki dacewa domin tsayar da shi a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

KU KARANTA:Malamai 4,692 za su rubuta jarabawar TRCN a Kaduna

Kungiyar ta fitar da wannan bayanan ne a cikin wani zancen da ya samu sanya hannun tsohon dan majalisar tarayya, Samson Osagie da kuma tsohon kakakin majalisar jihar Edo, Thomas Okosun.

Jawabin nasu kuwa yazo ne a daidai lokacin da Gwamna Obaseki ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar gwamnan Edo a karo na biyu wanda yayi ranar Laraba 2 ga watan Oktoba a Benin babban birnin jihar.

A cikin zancen kungiyar, sun fadi cewa gwamnan bai cancanci a sake zabensa saboda bai taka wata rawar a zo a gani ba bangaren cigaban jihar. Haka kuma bai iya amfani da dubarun jagoranci ba domin hadin kan ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar.

Zancen ya kara da cewa: “Gwamna Obaseki ya gaza wurin cika burin al’ummar Edo, saboda akwai ayyuka da dama wadanda a fitar da kudinsu amma ba ayi ko daya daga cikinsu ba.”

https://www.vanguardngr.com/2019/10/obaseki-you-dont-deserve-a-second-term-you-failed-us-edo-apc-group/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel