Malamai 4,692 za su rubuta jarabawar TRCN a Kaduna

Malamai 4,692 za su rubuta jarabawar TRCN a Kaduna

Hukumar tantance malaman Najeriya wato TRCN a ranar Juma’a 4 ga watan Oktoba 2019 ta ce malamai 4,692 ne za su rubuta jarabawa a jihar Kaduna domin gwada cancantarsu.

Kabir Yar’adua, shugaban TRCN reshen jihar Kaduna ne ya fitar da wannan sanarwa a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN, inda ya ce a cibiyoyi uku za’a rubuta jarabawar.

KU KARANTA:Jami’ar ABU Zaria na neman wanda zai maye gurbin Farfesa Ibrahim a matsayin shugaban jami’ar yayin da wa’adinsa ya kusa karewa

Ya kuma kara da cewa jarabawar wadda za a gabatar a kasa gaba daya za ta zo ne a ranar Asabar 12 ga watan Oktoba kuma za ayi amfani da na’ura mai kwakwalwa ne domin rubuta jarabawar.

Malaman dake zango na uku wato Zone 3 a Kaduna zasu rubuta jarabawarsu ne a Kwalejin Ilimi ta jihar Kaduna dake Gidan Waya, a cewarsa.

Haka kuma a kididdigar da ya bamu, ya sanar damu cewa malamai 3,820 ne na makarantun firamare yayin da 361 kuwa su ne na makarantun sakandare.

Bugu da kari, akwai mutum 22 wadanda ke karantarwa a makarantun gaba da sakandare yayin da wasu 489 ke rike da shahadar malaman makaranta amma ba koyarwa suke yi ba.

Yar’adua ya ce: “Idan har muka kammala wannan jarabawa cikin nasara, hakan zai daga yawan malamai masu shaidar TRCN zuwa 63, 128 a jihar Kaduna.”

Shugaban ya bayyana mana cewa hukumar TRCN ta riga ta yiwa malamai 58, 436 rajista a jihar Kaduna. Wannan dalilin ne ya sanya jahar ke sahun gaba a jerin sunayen jihohin dake da malamai masu dauke da rajistar hukumar TRCN, inji Yar’adua.

https://www.vanguardngr.com/2019/10/4692-teachers-set-for-trcn-professional-examination-in-kaduna/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel