Jami’ar ABU Zaria na neman wanda zai maye gurbin Farfesa Ibrahim a matsayin shugaban jami’ar yayin da wa’adinsa ya kusa karewa

Jami’ar ABU Zaria na neman wanda zai maye gurbin Farfesa Ibrahim a matsayin shugaban jami’ar yayin da wa’adinsa ya kusa karewa

Majalisar gudanarwar Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria ta bude kofar neman gurbin shugabancin jami’ar wato Vice Chancellor (VC), kasancewar wa’adin shugaban dake bisa kujerar a yanzu zai kare a watan Afrilun 2020.

Majiyar Daily Trust ta ruwaito cewa majalisar gudanawar ta fitar da wannan sanarwar ne a ranar Alhamis 3 ga watan Oktoba, 2019 inda ta bada dama ga masu sha’awar rike wannan mukamin daga ciki da wajen jami’ar da su garzayo domin mika takardunsu.

KU KARANTA:Gwamnatin jihar Ekiti ta horar da malamai 3,000

Jami’ar ABU a matsayinta na daya daga cikin manya-manyan jami’o’in yakin nahiyar Afirka dake makwabtaka da sahara na da dimbin Farfesoshin da zasu iya cike wannan gurbin ma mukamin VC.

Haka kuma, banda mutanen da ake sa ran zasu nemi wannan mukami daga wajen jami’ar, ana hasashen cewa wani daga cikin ‘yan cikin jami’ar ne zai dare bisa wannan mukami.

Sunan mutum guda wanda kowa ke tunanin shi zai gaji ragamar shugabancin shi ne, Farfesa Kabiru Bala na sashen Ilimin gine-gine, wanda kuma ya taba rike mukamin mataimakin shugaban jami’ar mai lura da ayyuka.

Sauran kuwa sun hada da; Farfesa Sadiq Zubairu Abubakar wanda shi ne wanda ke rike da mukamin mataimakin shugaban jami’ar mai lura da ayyuka a yanzu haka da Farfesa Zakari Mohammed wanda ya taba rike mukamin shugaban dakin karatu na jami’ar.

Bugu da kari akwai, Farfesa Hudu Abdullahi na sashen kimiyyar siyasa, Farfesa Bakari Adamu Girei tsohon shugaban tsangayar ilimin kiwon lafiya da dai sauransu.

https://www.dailytrust.com.ng/abu-searches-for-new-vice-chancellor.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel