Jaruma Fati Washa ta sha tofin Allah tsine a wajen masoyanta bayan ta wallafa wani hotonta na tsiraici

Jaruma Fati Washa ta sha tofin Allah tsine a wajen masoyanta bayan ta wallafa wani hotonta na tsiraici

- Wasu hotuna da jaruma Fati Washa ta wallafa a shainta na sada zumunta sun bar baya da kura

- Jarumar ta wallafa wannan hotuna ne a ranar Talatar nan da ta gabata domin nuna murnar ta da zagayowar ranar samun 'yancin kan Najeriya

- To sai dai mutane sun ta faman tofin Allah tsine akan wannan hotuna ganin cewa surar jikinta ta fili karara

A ranar bikin samun 'yancin kai na Najeriya da aka yi ranar Talata 1 ga watan Oktobar nan, mutane da jarumai da yawa sun fito sun nuna farin cikinsu da zagayowar wannan rana, inda suka dinga yin shiga dake nuna farin ciki, wajen sanya kaya masu nuni da alamar Najeriya.

A irin haka ne sai aka hango hotunan jaruma Fati Washa sun fara yawo a shafukan sada zumunta, inda tayi ado sanye da kaya masu launin kore da fari, ma'ana masu kama da tutar Najeriya.

To sai dai kuma wannan hoto da jarumar ta sanya ya jawo kace nace a wajen al'umma inda mutane da yawa suka dinga to fa albarkacin bakinsu akan wannan hoto da jaruma ta sanya.

Hoton dai kuru-kuru ya fito da surar jikinta, inda mutane da yawa daga cikin mabiyanta suka bayyana cewa jarumar ba ta sanya rigar nono ba, ma'ana ta dauki hoton ba tare da rigar nono ba, sannan kuma gashin kanta ya fito kowa yana kallo.

KU KARANTA: Hotuna: Wata tsaleliyar budurwa ta auri kare a kasar Indiya

Wannan hoto dai ya jawo kace nace a shafukan sada zumunta, inda mutane kowa ke ganin dama jaruman sun saba irin wannan shiga kawai dai Allah ne yayi ita na ta ya fito fili.

Har ya zuwa yanzu dai jarumar ba ta fito ta yi magana akan wannan abu da tayi ba, domin kuwa lokaci ya riga ya kure hotunan sun riga sun gama bazuwa a shafukan sadarwa na zamani.

Idan ba a manta ba kwanakin baya mun kawo rahoton yadda mujallar Fim Magazine ta zargi jaruma Rahama Sadau da amfani da mazaunan roba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel