Kashi 80 na yaran da ke mutuwa a Najeriya yan Arewa ne - Hukumar kididdigan Najeriya

Kashi 80 na yaran da ke mutuwa a Najeriya yan Arewa ne - Hukumar kididdigan Najeriya

Hukumar kididdigan Najeriya ta bayyana cewa kashi 80 na mutuwan yara yan kasa da shekaru biyar da haihuwa a Arewa yake faruwa.

Yayin jawabi a taron VASA da aka shirya a Akwanga jihar Nasarawa, shugabar hukumar kididdigar yan kasa wato NPA, Bimbola Salu-Hundeyin, ta ce bincike ya nuna cewa yara 2601 yan kasa da shekaru biyar suke mutuwa a Arewa kowani shekara sabanin 614 da ke mutuwa a kudu.

Salu-Hundeyin ta ce taron VASA na 2019 wanda ya kasance na biyu zai yi bincike domin gano abubuwan da ke sabbaba mutuwan yara yan kasa da shekaru biyar a Najeriya cikin shekaru biyar da suka gabata.

Tace: "Hukumar kididdigan Najeriya za tayi amfani da wannan taron domin gudanar da bincike kan mutuwan kananan yara domin taimakawa mahukunta wajen samar da dokoki a bangaren lafiya domin inganta rayuwar iyaye mata da yara a Najeriya,"

A wani labarin daban, Wata mumunar hadarin mota da ta uku da safiyar Juma'a ta hallaka akalla matasa uku a titin Oyemeku, Akure, jihar Ondo yayinda motarsu ta shiga cikin wata babbar motar da ke ajiye a bakin hanya.

Tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai NAN, shugaban hukumar kiyaye haduran hanya FRSC na jihar, Rotimi Adeleye, ya bayyana cewa hadarin ya faru ne tsakanin karfe 4:30 zuwa 5:00 na asuba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel