Ndume ya tunzura akan lamarin kara harajin kayayyaki

Ndume ya tunzura akan lamarin kara harajin kayayyaki

Tsohon Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Ali Ndume, a ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoba, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta ajiye shirinta na kara harajin kayayyaki daga kaso biyar cikin dari zuwa 7.2%. A cewar shi, shirin zai fi shafar talakawa.

Yayi magana tare manema labarai na fadar Shugaban kasa bayan wata ganawar sirri tare mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, a fadar Shugaban kasa, Abuja.

Sanata Ndume ya ce idan har gwamnati ta aiwatar da karin harajin kaya, toh kuwa talaka ne zai shiga halin ni-'ya-su ta yadda farashin komai a kasuwa zai daga kama daga farashin mai da magani da mota da abinci.

Sai dai kuma Ndume ya goyi bayan kara harajin masu amfani da waya.

A cewar Ndume, mutane kusan miliyan 60 ne suke amfani da waya a Najeriya wanda a ganinsa, wannan ce hanya mafi sauki da gwamnati za ta tara kudade.

KU KARANTA KUMA: Wulakanta Qur’ani: Gwamnatin Zamfara ta yi kira ga azumin kwana 3

A wani lamarin kuma, mun ji cewa hukumar kididdigan Najeriya ta bayyana cewa kashi 80 na mutuwan yara yan kasa da shekaru biyar da haihuwa a Arewa yake faruwa.

Yayin jawabi a taron VASA da aka shirya a Akwanga jihar Nasarawa, shugabar hukumar kididdigar yan kasa wato NPA, Bimbola Salu-Hundeyin, ta ce bincike ya nuna cewa yara 2601 yan kasa da shekaru biyar suke mutuwa a Arewa kowani shekara sabanin 614 da ke mutuwa a kudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel