Wulakanta Qur’ani: Gwamnatin Zamfara ta yi kira ga azumin kwana 3

Wulakanta Qur’ani: Gwamnatin Zamfara ta yi kira ga azumin kwana 3

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya yi kira ga al’umman Musulmi da su dauki azumin kwanaki uku sannan su gudanar da addu’o’i na musamman domin neman azabar Allah akan wadanda suka wulakanta littafin Al-Qur’ani mai tsarki a jihar.

Matawalle ya yi kiran ne a garin Gusau a ranar Juma’a, 4 ga watan Oktoba ta hannun darakta janar na labaransa, Malam Yusif Idris.

An sa samun rigingimu na wulakanta littafi Mai girma na Musulmai tun a shekarar 2016, musamman a Gusau, babbar birnin jihar.

Gwamnan yace hukuncin ya biyo bayan shawarar da aka samu daga kungiyar malamai kan cigaba da afkuwa lamarin.

“Ina rokon mutanen Zamfara da su gudanar da azumi na kwanaki uku sannan su yi addu’a ga Allah madaukakin sarki akan ya fallasa makirai a jihar,” inji shi.

Matawalle yace gwamnatin jihar ta shirya taron addu’a na musamman a filin masallacin idi na Gusau a ranar Juma’an nan.

Ya kuma yi kira Limaman masallatan Juma’a da su yi addu’o’i domin neman Allah ya shiga cikin lamarin.

KU KARANTA KUMA: Runduna sojin Najeriya ta sake gina rusasshen gadar ATBU da ya yi sanadiyar mutuwar dalibai 4

A ranar Juma’a da ya gabata ne aka tsinci fallayen Qur’ani a cikin najasa a makarantar Shatima Model Primary School Tudun-Wada, Gusau wanda yayi sanadiyar rufe makarantar da dakatar da dukkanin malaman da gwamnatin jihar tayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel