'Yan sanda sun kama wani fitaccen mai barkwanci saboda yada labaran karya a intanet

'Yan sanda sun kama wani fitaccen mai barkwanci saboda yada labaran karya a intanet

- 'Yan sandan babban birnin tarayya Abuja, sun kama mai barkwanci, Augustine Valentine da aka fi sani da MC Fine kan zarginsa da yada labaran karya

- Mai barkwancin 'ya ruwaito cewa an kama wata mai satar mutane yayin da ta ke yunkurin sace wani yaro alhalin matar tana fama da tabin hankali ne

- Daga baya Valentine cikin nadama ya bayyana cewa baya wurin a lokacin da abin ya faru

- Mutane da dama sun bayyana cewa matar da ake yiwa zargin mai satar mutane mai tabin hankali ce da aka sani a unguwar kuma ba ta barazana ga lafiyar kowa

Rundunar 'yan sanda a ranar Laraba 3 ga watan Oktoba sun kama wani fitaccen mai barkwanci, Augustine Valentine da aka fi sani da 'MC Fine' kan zarginsa da yada labaran karya.

DPO na 'yan sanda na unguwar Bwari a Abuja, Biodun Makanjuola ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewa Valentine ya wallafa rahoton a shafinsa na Facebook inda ya yi ikirarin cewa an kama wata mata mai satar mutane.

Ya ce, "Bayan da muka gudanar da bincike mun gano cewa karya ne."

Legit.ng ta ruwaito cewa an kaiwa matar mai matsakaicin shekaru mai suna Zulai hari a ranar 2 ga watan Oktoba kusa a Bwari kan zargin cewa tayi yunkurin sace wani yaro mai shekaru biyu.

'Yan sanda sunyi gagawa shiga tsakani suka kama matar kuma daga bisani suka gano cewa bata da cikaken lafiya kuma akwai alamun tana da tabin hankali.

DPO ya ce a yayin da 'yan sanda ke bincike, Valentine ya wallafa wani labarin karya kan lamarin a shafinsa na dandalin sada zumunta.

Ya ce, "Da aka kawo mana ita, na bayar da umurnin a kai ta asibiti domin duba lafiyarta. Sun dawo da rahoton likita da ke nuna cewa tana fama da tsananin damuwa.

"Rahoton ya ce a tafi da ita asibitin kwakwalwa na Karu domin zurfafa bincike. Yanzu muna shirin kai ta can.

"Muna kan wannan binciken ne sai aka fara kira na kan rahoton da aka wallafa a Facebook inda akayi ikirarin matar mai satar mutane ne. Rahoton ya yi ikirarin cewa an gano bayyanan adadin yara da dama da ta sace a cikin wayarta.

"Nayi bincike kuma na gano wanda ya fara wallafa labarin kuma na sa aka gayyato shi domin amsa tambayoyi inda ya amsa cewa ya kara 'gishiri' a labarin domin labarin ya yi dadi."

DPO ya nuna bacin ransa kan lamarin inda ya gargadi mutane su dena yada labaran da ba su tabbatar da abinda ya faru ba domin hakan na iya zama sanadiyar tayar da fitina.

Valentine ya nemi afuwa inda ya ce wani ne ya aiko masa da labarin a Whatsapp.

Mutane da dama mazauna unguwar sun yi wa matar shaida cewa ba a taba samun ta da aikata wani mummunan laifi ba kuma kowa ya san tana fama da tabin hankali amma ita mai son yara ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel