Rundunar sojin Najeriya ta sake gina rusasshen gadar ATBU da ya yi sanadiyar mutuwar dalibai 4

Rundunar sojin Najeriya ta sake gina rusasshen gadar ATBU da ya yi sanadiyar mutuwar dalibai 4

Rundunar sojin Najeriya ta sake gina rushahhen gadar jami’ar Tafawa Balewa wato ATBU wanda yayi sanadiyar mutuwar dalibai a jihar Bauchi.

An tattaro cewa Injiniyoyin sojoji da wasu jama’a ne suka hada hannu wajen sake gina gadar.

Dalibai na amfani da gadar daga dakunan kwanansu zuwa wuraren karatunsu.

Jami'an da aka gani a wajen ginin sun ki cewa komai akan lamarin amma dai ana ganin cewa runduna sojin Najeriya ce ta dauki nauyin aikin kai tsaye.

Da aka tuntubi daaktan hulda da jama'a na makaanta, Dr. Andee Iheme, yace: "rundunar sojin Najeriya na cika alkawarin da ta dauka na gina gada mai inganci a wajen ruwan".

Ya yi godiya ga hukumomin rundunar sojojin Najeriya akan cika alkawarinsu.

"Mun gode ya ku dakarun sojoji akan daukar alkawari na gaskiya. lallai kun nuna cewa ku yan Najeriya ne na gaskia wadanda a shirye suke su bayar da duk wani umurni da zai kawo cigaban Najeriya."

KU KARANTA KUMA: Ko ku daina zuwa sansanin NYSC ko kuma mu fara kama ku muna daurewa - Shugaban NYSC ya gargadi 'yan bautar kasar da basu cancanta ba

Dalibai hudu ne suka mutu yayinda wasu da dama suka jikkata a ranar 6 ga watanAgusta lokacin da gadar ya rufta sakamakon ruwan sama mai karfi da aka yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel