Da duminsa: Mumunar hadarin mota ya auku da safen nan, mutane uku sun hallaka (Hotuna)

Da duminsa: Mumunar hadarin mota ya auku da safen nan, mutane uku sun hallaka (Hotuna)

Wata mumunar hadarin mota da ta uku da safiyar Juma'a ta hallaka akalla matasa uku a titin Oyemeku, Akure, jihar Ondo yayinda motarsu ta shiga cikin wata babbar motar da ke ajiye a bakin hanya.

Tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai NAN, shugaban hukumar kiyaye haduran hanya FRSC na jihar, Rotimi Adeleye, ya bayyana cewa hadarin ya faru ne tsakanin karfe 4:30 zuwa 5:00 na asuba.

Adeleye ya ce mutane biyar abin ya shafa kuma jami'an hukumar FRSC sun kai gawawwakin wadanda suka hallaka a take dakin ajiye gawawwakin asibitin Akure.

Yace:"Su biyar ne cikin wata motar kirar Lexus kuma an samu labarin cewa suna dawowa ne daga taron banbadewa da safen nan yayinda suka shararo da gudun tsiya har suka shige cikin motar."

"Uku daga cikinsu sun mutu take a wajen yayinda sauran biyu na cikin halin kakanikaye,"

Adeleye, ya shawarci iyaye su rika tarbiyan yaransu saboda yaran da wannan abun ya shafa yan kasa da shekaru 20 ne da haihuwa.

Da duminsa: Mumunar hadarin mota ya auku da safen nan, mutane uku sun hallaka (Hotuna)
Motar
Asali: Facebook

KU KARANTA: Gwamnatin za ta sallami ma'aikata muddin ana son ta biyan mafi karancin albashi - Chris NgigE

Da duminsa: Mumunar hadarin mota ya auku da safen nan, mutane uku sun hallaka (Hotuna)
Daya daga cikin matasan
Asali: Facebook

Da duminsa: Mumunar hadarin mota ya auku da safen nan, mutane uku sun hallaka (Hotuna)
Da duminsa: Mumunar hadarin mota ya auku da safen nan, mutane uku sun hallaka (Hotuna)
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel