Fusatattun matasa sun kashe jami'in VIO a Neja

Fusatattun matasa sun kashe jami'in VIO a Neja

Rundunar 'yan sandan reshen jihar Neja ta ce wasu fusatattun masu zanga-zanga sun kashe wani Ahmadu Bello, jami'in VIO a karamar hukumar Mariga na jihar.

Kwamishinan 'yan sanda, Alhaji Adamu Usman ne ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) a ranar Juma'a a Minna.

"A ranar 3 ga watan Oktoba misalin karfe 1.30 wani jami'in VIO ya tsayar da wasu matasan Fulani uku masu suna Malami Mohammed, Juli Musa da Dawa Ali 'yan asalin kauyen Oro da ke karamar hukumar Mariga saboda ya same su da babbur kirar Bajaj mara rajista amma ba su tsaya ba.

"Jami'in VIO din ya bi su kuma garin gudu a kan babur din sai suka yi karo da wata trela mai lamba FKJ 512 XW da ke zuwa daga Tegina-Kampani Bobi. Dukkansu uku sun mutu nan take.

DUBA WANNAN: Gwamnan PDP ya umarci a mayar da sunan Sardauna a titin da aka sauya da sunansa

"Da ya ga abinda ya faru, marigayin jami'in na VIO ya juya domin ya koma ofishin 'yan sanda na Bobi amma wasu fusatattun matasa suka bi shi suka kashe shi," inji Kwamishinan.

Ya ce tuni an aike da karin jami'an tsaro daga Kontagora zuwa kauyen domin tabbatar da zaman lafiya.

Kwamishinan ya gargadi al'umma su guji daukan doka a hannunsu domin duk wanda aka kama ya aikata hakan zai fuskanci shari'a.

"Ba za mu amince da wani abinda zai iya kawo hayaniya da tashin hankali ba duba da cewa akwai doka da aka kafa domin tabbatar da zaman lafiya tsakanin al'umma," inji Kwamishinan 'yan sandan.

Shugaban 'yan sandan ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu da hannu cikin kisar zai fuskanci fushin hukuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel